Jigawa: Ma'aikata Za Su Tsunduma Yajin Aiki kan Rashin Biyan Sabon Albashin N70000
- 'Yan kwadago a Jigawa sun umarci ma’aikata da su fara yajin aiki kan rashin biyan sabon albashin N70,000 da aka amince da shi
- Shugabannin NLC da TUC sun bayyana cewa gwamnatin jihar ta gaza cika wa’adin biyan sabon mafi ƙarancin albashin da aka bata
- Duk da amincewa da sabon tsarin albashin na N70,000, NLC ta ce za a fara yajin aiki daga 1 ga Disamba idan har ba a fara biya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jigawa - NLC reshen Jigawa ta ayyana yajin aikin sai baba ta gani kan gazawar gwamnatin jihar na aiwatar da mafi karancin albashin N70,000 da aka amince da shi.
Sanarwa daga Sunusi Alhassan (NLC) da Bashir Tijjani Abubakar (TUC) ta umarci ma'aikatan jihar da su shirya tsunduma yajin aikin.
NLC ta soki gwamnatin jigawa kan albashi
An bukaci kungiyoyin kwadago da su fara shiri don shiga yajin aiki idan har gwamnatin ba ta fara biyan N70,000 kafin karshen Nuwamba ba, inji rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NLC ta tabbatar da amincewa da albashin N70,000 a jihar, amma ta ce abin takaici ne yadda gwamnatin jihar ke jinkirin fara aiwatar da shi.
The Guardian ta rahoto cewa matsayar ta fito ne daga taron hadin gwiwar kwamitin zartarwa da aka gudanar ranar 18 ga Nuwamba, 2024, a Labour House, Dutse.
NLC za ta tsunduma yajin aiki a Jigawa
Duk da jiran rattaba hannu kan yarjejeniyar, NLC ta jaddada wajibcin bin umarnin kungiyar ta kasa ta bukaci jihohin da ba su aiwatar da sabon albashin ba su shiga yajin aiki.
Shugabannin kwadago na Jigawa sun sanar da gwamnati shirinsu na kammala yarjejeniyar don tabbatar da aiwatar da sabon albashin, kuma suna jira suji daga gareta.
Shugabannin NLC da TUC sun tabbatar da cewa za su bi umarnin uwar kungiyar na shiga yajin aiki daga ranar 1 ga Disamba, domin kare hakkin ma’aikatan Jigawa.
Asali: Legit.ng