'Zai Haddasa Rikici': Dattawan Arewa Sun Gargadi Tinubu kan Sake Fasalin Haraji

'Zai Haddasa Rikici': Dattawan Arewa Sun Gargadi Tinubu kan Sake Fasalin Haraji

  • Dattawan Arewaci sun nuna adawa ga dokar gyaran haraji, suna masu kallonta a matsayin dokar da aka tsara da muguwar niyya
  • Kungiyar NEF ta ƙalubalanci rashin shigar da masu ruwa da tsaki a cikin aiwatar da dokar, musamman majalisar tattalin arziki
  • NEF ta yi kira ga shugabannin Arewa da su fito su nuna adawarsu, yayin da ta yi gargadin cewa dokar za ta iya kawo rabuwar kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar dattawan Arewacin Najeriya (NEF) ta ki amincewa da Dokar Gyaran Haraji, tana mai kallonta a matsayin dokar da aka tsara da muguwar niyya.

NEF ta soki yadda aka tsara dokar, tana mai cewa ba a tuntubi wasu muhimman masu ruwa da tsaki, ciki har da 'yan majalisar tattalin arziki yayin shirya dokar ba.

Kara karanta wannan

Dalibai sun cire tsoro, sun fadawa Tinubu manyan matsaloli 2 da ke addabar Najeriya

Dattawan Arewa sun yi magana kan sabuwar dokar sake fasalin haraji
Dattawan Arewa sun gargadi Tinubu kan aiwatar da dokar sake fasalin haraji. Hoto: Ango Abdullahi, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Dattawan Arewa na adawa da dokar haraji

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shugaban NEF, Farfesa Ango Abdullahi, ya bayyana damuwar kungiyar kan wannan doka a wata takardar bayan taro da ya fitar a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan taron kwamitin amintattu na NEF, Abdullahi Ango ya yi gargadi game da manufofin shubuhohi da ka iya kara nakasa albarkatun Arewa

Kungiyar ta yaba da matsayin gwamnonin Arewacin Najeriya da majalisar sarakunan gargajiya na Arewa kan kin yarda da dokar, tana ganin hakan na da ‘yanci.

NEF ta gargadi Tinubu kan dokar harajin

Dattawan Arewa sun bukaci ‘yan siyasar Arewa a majalisar tarayya da su nuna kin amincewarsu da dokar, suna masu nuna barazanar da sake fasalin ke da shi ga hadin kan kasa.

“Taron ya yi nuni da cewa, akwai mummunan kuduri a dokar sake fasalin haraji da aka gabatar, kuma barazana ce ga hadin kanmu da hadin kan kasa."

Kara karanta wannan

'Ko sai kowa ya mutu ne,' Dattawan Arewa sun yi raddi ga Tinubu kan tsadar rayuwa

- A cewar NEF.

Kungiyar dattawan ta nuna takaicinta kan yadda yawancin ‘yan siyasar Arewa a majalisar tarayyar suka ki fitowa a fili su soki wannan doka.

NEF ta zargi Dokar Gyaran Haraji da aka gabatar cikin sauri ba tare da la’akari da ra’ayoyin masu ruwa da tsaki ba, tana mai jaddada cewa akwai mummunar niyya a hakan.

NEF ta soki harajin 0.5% na CBN

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar Dattawa Arewa ta yi martani kan sabon matakin da Babban Bankin Najeriya, CBN ya kawo na biyan harajin 0.5%.

Kungiyar ta yi fatali da matakin inda ta bukaci gwamnatin kasar ta sake tunani kan lamarin saboda halin matsin tattalin arziki da 'yan ƙasar ke ciki a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.