Dalibai Sun Cire Tsoro, Sun Fadawa Tinubu manyan matsaloli 2 da ke addabar Najeriya
- Kungiyar daliban Najeriya (NANS) ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta daukar matakan magance yunwa da talauci
- Abdulyekinn Odunayo, sakataren a NANS, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta kara jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin hali
- Ya kuma yi kira ga shugaban kasar da ya sake tsara manufofin tattalin arziki dommin rage wahalar rayuwa da farashin kayayyaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar daliban Najeriya (NANS) ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta magance yunwa da wahalar tattalin arziki a kasar nan.
NANS ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakataren majalisar dattawan kungiyar, Abdulyekinn Odunayo, ya sanya wa hannu a ranar Asabar.
NANS ta fadawa Tinubu matsalolin Najeriya
Odunayo ya ce tun bayan hawan Shugaba Tinubu, ‘yan Najeriya ke fama da talauci da yunwa, inda ya ce akwai bukatar ya sauya manufofin tattalin arziki, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa cire tallafin mai da tuttula kudin Naira a kasuwannin hada hada sun kara jefa ‘yan Najeriya cikin matsin tattalin arziki mai tsanani.
Ya lura cewa yawancin ‘yan Najeriya sun yi fatan gwamnati mai ci za ta magance matsalolin tattalin arziki da aka gada daga gwamnatin baya.
Dalibai sun ba Tinubu shawarar mafita
Sai dai, ya ce maimakon haka, farashin kayan masarufi da sauran kayayyakin yau da kullum sun yi tashin gwauron zabi, inda wasu suka fara gagarar talaka.
Odunayo ya ce dalibai ma ba su tsira daga wannan hali ba, domin yawanci sun daina karatu saboda matsalar tattalin arziki na rashin biyan kudin makarantar.
Punch ta rahoto kungiyar NANS ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya aiwatar da manufofi na gaggawa kuma 'yan tsaka-tsaki domin rage wahalar da ‘yan kasa ke fuskanta.
NANS ta lissafawa Tinubu bukatunta
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar Daliban Najeriya (NANS) reshen Kudu maso Yamma ta lissafo abubuwan da ta ke bukatan Shugaba Tinubu yafi bai wa muhimmanci.
NANS ta nemi Tinubu da ya kawo ayyukan raya kasa da samar da aikin yi, tare da rokon shugaban kasar da ya kare dalibai da malamansu a lokacin da suke makaranta.
Asali: Legit.ng