Asiri Ya Tonu: Yadda Aka Bankado Badakalar Kwangilar N197bn a Ma'aikatun Tarayya
- Rahoton mai binciken kudi na tarayya ya bayyana biyan kudaden kwangila na sama da N197.72bn ba tare da bin ka’ida ba
- Babban mai binciken ya bankado badakalar kwangilolin da ba a kammala ba ko wadanda ba a aiwatar ba, da suka kai N167.59bn
- Rahoton ya kuma yi bayanin yadda aka karya dokokin tsarin saye da sayarwa a hukumomi 32, inda aka saba ka’idojin ba da kwangila
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wani rahoto da babban mai binciken kudi na tarayya ya fitar, ya bayyana yadda aka tafka badakalar kwangila da ta kai ta N197.72bn a ma’aikatu, da hukumomi.
Rahoton, wanda ya kunshi ayyuka tsakanin 2020 da 2021, ya nuna gazawar tsari a cikin biyan kuɗi da kuma keta dokokin sayayya a cikin hukumomi da dama.
An bankado badakalolin kwangila a ma'aikatu
Rahoton Punch ya ce binciken ya bankado kura-kurai a cikin kwangilolin da darajarsu ta kai N7.39bn a cikin hukumomi da ma'aikatu 32, da suka saba wa ka’idojin kudi na 2009.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar da ke kula da wutar lantarki ta karkara ta nuna rashin bin ka’ida mafi girma na N2.12bn, yayin da aka tafka badakalar N11.72 a kamfanin buga kudi na Najeriya.
Wani binciken kuma ya nuna cewa an biya N167.59bn na wasu kwangilolin da aka ki kammala su ko ma ba a aiwatar da su ba, wanda ya saba wa ka’idojin hada-hadar kudi.
Wasu badakalolin N100bn, N20.33bn da N2.41bn
Kamfanin Dillancin Wutar Lantarki na Najeriya ya samu N100bn daga cikin wadannan kudade, yayin da Cibiyar Raya Mata ta Kasa ta samu mafi karancin kudin na N2.17m.
An kuma gano badakalar kudi da aka yi a cikin kwangiloli da ta kai N20.33bn, inda aka tafka badakalar N14.14bn a hukumar NSPM, wanda shi ne mafi girma a wannan fanni.
Bugu da kari, an biya N2.41bn kan kwangilolin da suka zarce ka’idojin da aka amince da su ba tare da samun satifiket daga ofishin kula da harkokin gwamnati ba, wanda ya shafi hukumomi biyar.
ICPC na binciken badakalar kwangilar NSITF
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar ICPC ta titsiye Chris Ngige, daya daga cikin ministocin gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
An ce ICPC ta yi wa Chris Ngige, wanda ke kula da ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi tambayoyi kan zargin ya taka rawa a badakalar kwangiloli da daukar aiki.
Asali: Legit.ng