Hukumar EFCC ta sake bankado wata sabuwar badakalar kudin makamai

Hukumar EFCC ta sake bankado wata sabuwar badakalar kudin makamai

Hukumar EFCC ta gano wata sata da ake zargin an tafka na makudan kudin kwangila da aka bada domin shigo da makamai daga shekarar 2008 zuwa 2015 a Najeriya.

Jaridar Leadership ta fitar da rahoto cewa Ma’aikatar tsaro ta samu damar cin bashin Naira biliyan 35 domin sayen makamai da kayan aiki a shekarun da su ka wuce.

Rahotannin jaridar sun bayyana cewa Ma’aikatar ta samu wannan dama daga ofishin kula da bashin Najeriya (DMO), kuma har an fitar da duk kudin wannan kwangila.

Kamfanonin da ake zargi da yin awon gaba da kudin kwangilar makaman a Najeriya sun hada da: Richfield Technologies Ltd, VTB Export and Import Ltd; da Freerose Ltd.

Ana kuma zargin cewa akwai wani kamfani mai suna Africa Integrated Services Limited da cewa ya karbi kudin shigo da makamai cikin kasar amma ya yi gaba da kudin.

KU KARANTA: EFCC ta koma kotu da wanda ake zargi da satar kudin makamai

Hukumar EFCC ta sake bankado wata sabuwar badakalar kudin makamai
EFCC ta na zargin an wawuri N35b da sunan kudin shigo da makamai
Asali: UGC

Akwai wani kamfanin da aka ba kwangilar shigo da na’urorin sadarwa na kudi N1, 020, 287, 357, da kuma manyan motoci na N50, 000. 000 da wasu maguna na miliyoyi.

Haka zalika an ba wannan kamfani kwangilar shigo da gingimarin motoci na N85, 000, 000 da wasu na’urori wanda aka warewa kudin da ya haura Naira Biliyan 1.1.

Wannan kamfani ya kuma samu kwangilar shigo da makamai da harsashi na Naira miliyan 533 da miliyan 778. Tony Orilade ya ce ana binciken wannan badakalar kudi.

Takardun da su ka shiga hannun Jaridar ya nuna cewa wani tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa da tsofaffin Ministocin tsaro su na da hannu a badakalar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng