Gombe: An Shiga Alhini da Tsohon Shugaban PDP Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Gombe: An Shiga Alhini da Tsohon Shugaban PDP Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Tsohon gwamnan Gombe, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo ya sanar da rasuwar tsohon shugaban PDP a jihar
  • Dankwambo ya nuna alhini kan rashin tsohon shugaban jam'iyyar a karamar hukumar Gombe, Alhaji Idris Bello
  • Sanatan daga bisani ya tura sakon ta'azziya ga iyalan marigayin da yan uwansa da abokan arziki inda ya yi masa addu'ar samun rahama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - An shiga alhinin babban rashi na jigo kuma tsohon shugaban jam'iyyar PDP a jihar Gombe.

Marigayin ya rike shugabancin jam'iyyar PDP a matakin karamar hukumar Gombe da ke Arewacin Najeriya.

Tsohon shugaban PDP a Gombe ya yi bankwana da duniya
Sanata Ibrahim Dankwambo ya sanar da rasuwar tsohon shugaban PDP a Gombe. Hoto: Legit.
Asali: Original

Gombe: Dankwambo ya jajanta rasuwar jigon PDP

Tsohon gwamnan Gombe kuma Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo shi ya tabbatar da mutuwar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

An shiga jimami da tsohon sanata a Kano ya riga mu gidan gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Dankwambo ya nuna alhini bisa rasuwar marigayin inda ya ce tabbas an yi babban rashin hazikin mutum a Gombe.

Tsohon gwamnan ya tura sakon ta'azziya ga iyalansa da yan uwa da abokan arziki kan wannan rashin da aka yi.

Dankwambo ya yi addu'ar rahama ga jigon PDP

"Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, cikin alhini, tare da mayar da dukkan lamura ga Allahu subhanahu wa ta’ala (SWT), na samu labarin rasuwanr Alhaji Idris Bello, wato Alhaji Yaro Na Gambo Isari, shugaban Jam'iyyar PDP na karamar hukumar Gombe da ya gabata."
"Babu shakka mun yi rashin abokin tafiya, masoyi mai jajircewa da tsananin nuna kishin al'umma, mai sauƙin kai da karamci."
"Shugabancin da yayi mana a jam'iyyar PDP na shekara hudu a karamar hukumar Gombe ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarori, babu shakka rashinsa zai haifar da giɓi mai wahalar cikewa, ina mika sakon ta'aziyya ga iyalansa da yan uwansa da abokan arziki."

Kara karanta wannan

Ba a gama da zargin rigima tsakaninsu ba, Kanin Kwankwaso ya maka Abba a kotu

"Ina rokon Allah SWT ya jikansa da rahama, ya ba shi aljannatul Firdausi, ya albarkaci bayansa."

- Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo

Malamin Musulunci ya rasu a Gombe

Kun ji cewa an sanar da rasuwar shahararren malamin addinin Musulunci, Gwani Muhammad Sani a jihar Gombe.

An ruwaito cewa Sheikh Gwani Muhammad Sani ya shafe shekaru yana karantar da ɗalibai Alkur'ani daga dukkan sassan Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.