Tura Ta Kai Bango, Matasan N Power Za Su Fantsama Tituna kan Albashin Watanni 9
- Kungiyar matasa da suka ci gajiyar N-Power ta shirya gudanar da zanga-zanga kan basukan da suke bin gwamnati
- Matasan sun nuna damuwa kan yadda gwamnatin ta ki biyansu hakkokinsu na watanni tara duk da kokarin shawo kan lamarin
- Shugaban kungiyar, Kwamred Muhammad Abubakar Habibu GMB shi ya bayyana haka ga jaridar Legit Hausa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Matasan da suka ci gajiyar N-Power sun shirya fara zanga-zanga kan basukan da suke bin Gwamnatin Tarayya.
Matasan sun koka kan yadda gwamnatin ta yi fatali da su duk da kokarin neman hakkinsu da suka yi a lokuta da dama.
Matasan N-Power sun gaji da yaudarar Tinubu
Shugaban kungiyar, Kwamred Muhammad Habibu Abubakar GMB shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya turawa wakilin Legit Hausa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamred GMB ya ce sun yanke shawarar fara zanga-zanga daga ranar 2 zuwa 6 ga watan Disambar 2024 a birnin Abuja.
"Wannan kungiya tana wakiltar matasan N-Power da aka rike musu kudinsu na tsawon watanni takwas zuwa tara duk da kokarin nemo hanyoyin shawo kan lamarin amma ba a samu biyan bukata ba."
- Kwamred Muhammad Habibu GMB
Matasan N-Power sun yanke shawarar fara zanga-zanga
"Duba da rashin samun biyan bukata, mun yanke shawarar fara zanga-zanga daga ranar 2 zuwa 6 ga watan Disambar 2024 daga Majalisar Tarayya zuwa ma'aikatar jin kai da walwala har zuwa ofishin kungiyar yan jaridu ta NUJ."
"Za a fara gudanar da zanga-zangar da misalin karfe 10.00 na safe zuwa karfe 2.00 na rana."
- Kwamred Mubammad Habibu Abubakar GMB
Legit Hausa ta tattauna da wani dan N-Power
Wani da ya ci gajiyar N-Power, Musa Muhammad Adamu ya ce wannan mataki abin farin ciki ne matuka.
Musa ya ce shi ma yana daga cikin masu bin gwamnatin basukan watanni takwas amma har yanzu shiru.
Ya yabawa shugabannin kungiyar inda ya ce suna yi musu fatan alheri da samun abin ake bukata.
Tinubu zai biya matasan N-Power bashinsu
A baya, kun ji cewa an fara ƙoƙarin ganin gwamnatin tarayya ta biya bashin da matasan Najeriya yan N-Power suka biyo gwamnatin da ta gabata.
Tawaga da ta hada da bangarorin gwamnati da yan N-Power ta gana a birnin tarayya Abuja domin duba yadda za a biya matasan.
Wannan ya biyo bayan yin wani zama na musamman tsakanin matasan N-Power da wakilan gwamnatin tarayya a Abuja.
Asali: Legit.ng