Gwamna Buni Ya Amince da Sabon Mafi Karanci Albashi, Ya Fadi Lokacin Fara Biya
- Gwamnan jihar Yobe ga amince da sabon mafi ƙarancin albashin da za a riƙa biyan ma'aikatan gwamnati
- Mai Mala Buni ya amince da mafi ƙarancin albashi na N70,000 wanda za a fara biyan ma'aikatan gwamnatin jihar daga watan Disamban 2024
- Amincewa da sabon mafi ƙarancin albashin ya biyo bayan miƙa rahoton kwamitin da aka kafa domin sabon albashin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Yobe - Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan gwamnatin jihar.
Gwamna Mai Mala Buni ya amince da fara biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000 daga watan Disamba.
Buni ya amince da sabon albashi
Mai magana da yawun gwamnan, Mamman Mohammed ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mamman Mohammed ya ce amincewar ta biyo bayan shawarar da kwamitin mafi ƙarancin albashi da gwamnatin jihar ta kafa ya ba da, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Kwamitin ya ba da shawarar daidaita kuɗaɗen ƙananan hukumomi don tabbatar da mayar da su kan sabon tsarin mafi ƙarancin albashin daga tsohon wanda ake biya a baya.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun bakin ya fitar, ana sa ran kammala tsarin nan ba da jimawa ba domin amincewa da shi ta yadda za a fara biyan ma'aikatan ƙananan hukumomin sabon albashi.
Gwamnati na sa ran ma’aikatan gwamnatin jihar za su ƙara jajircewa wajen gudanar da ayyukansu sakamakon amincewa da sabon tsarin albashin.
Karanta wasu labaran kan mafi ƙarancin albashi
- "Ba gudu ba ja da baya," NLC ta gargaɗi gwamnoni kan sabon mafi ƙarancin albashi
- Gwamma ya kere N70,000, ya faɗi sabon albashin da zai fara biyan ma'aikata
- Gwamna ya sanar da sabon albashin da zai fara biyan ma'aikata, ya yi ƙarin fansho
Gwamna Zulum ya yi ƙarin albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya amince da ƙarin albashi ga likitocin da ke aiki a ƙarƙashin gwamnatin jihar.
Gwamna Zulum ya amince a yi wa likitocin ƙari su koma suna karɓar albashi iri ɗaya da abinda ake biyan takwarorinsu a matakin tarayya.
Asali: Legit.ng