An Shiga Jimami da Tsohon Sanata a Kano Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Fitaccen dan siyasa a jihar Kano, Sanata Aminu Inuwa ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya
- Marigayin ya rike muƙamin sanata a jamhuriya ta uku karkashin jam'iyyar SDP bayan rasa tikitin takarar gwamna
- Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a jiya Juma'a 22 ga watan Nuwambar 2024 yana da shekaru 79
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - An yi rashi a jihar Kano bayan sanar da rasuwar fitaccen dan siyasa kuma tsohon sanata.
Marigayin Sanata Aminu Inuwa ya rasu ne a jiya Juma'a 22 ga watan Nuwambar 2024 bayan fama da jinya.

Source: Original
Kano: Takarar marigayin a karkashin jam'iyyar SDP
Marigayin ya yi suna ne bayan fitowa takarar gwamna karkashin jam'iyyar SDP a jamhuriya ta uku, cewar Daily Nigerian.
Sanata Inuwa ya rasa tikitin tsayawa takarar ga Magaji Abdullahi a wancan lokaci sai dai ya yi nasara a takarar Sanatan Kano ta Tsakiya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ya bar mata da yara da kuma tulin jikoki a rayuwarsa.
An haifi Sanata Inuwa a ranar 15 ga watan Disambar 1945 inda ya yi karatun firamare a Gidan Makama.
Mukaman da Sanata Inuwa ya rike a rayuwarsa
Daga bisani, marigayin ya koma Kwalejin Rumfa da ke Kano da kuma Kwalejin Barewa da ke birnin Zaria a jihar Kaduna.
Sanata Inuwa ya rike muƙamin shugaban hukumar sadarwa ta NITEL inda aka karrama shi saboda sauyin da ya kawo.
Har ila yau, Sanatan ya rike shugaban Sure-P da kamfanin Kandama da kuma gidan gona na Tiga.
Kanin Kwankwaso ya maka Abba a kotu
Kun ji cewa dan uwan Sanata Rabi'u Kwankwaso ya maka Gwamna Abba Kabir a kotu kan takaddamar fili a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya.
Mutumin mai suna Garba Musa Kwankwaso wanda kani ne a wurin tsohon gwamnan ya bukaci kotun da dakatar da gwamnan.
Wannan na zuwa ne bayan zargin takun-saka tsakanin Abba da mai gidansa, Rabiu Kwankwaso kwanakin baya wanda gwamnan ya musanta.
Asali: Legit.ng

