Ba a Gama da Zargin Rigima Tsakaninsu ba, Kanin Kwankwaso Ya Maka Abba a Kotu
- Dan uwan Sanata Rabi'u Kwankwaso ya maka Gwamna Abba Kabir a kotu kan takaddamar fili a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya
- Mutumin mai suna Garba Musa Kwankwaso wanda kani ne a wurin tsohon gwamnan ya bukaci kotun da dakatar da gwamnan
- Wannan na zuwa ne bayan zargin takun-saka tsakanin Abba da mai gidansa, Rabiu Kwankwaso kwanakin baya wanda gwamnan ya musanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir ya gamu da matsala bayan maka shi a kotu da kanin Sanata Rabi'u Kwankwaso ya yi.
Garba Musa Kwankwaso wanda kani ne ga Sanatan ya maka Abba Kabir da wasu kan takaddamar fili a jihar.
An shigar Abba Kabir kara a kotu
Daily Nigerian ta ruwaito cewa daga cikin wadanda ake karar akwai kwamishinan shari'a a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran sun hada da kwamishinan filaye da safiyo na jihar Kano da kuma hukumar tsara birane ta KNUPDA.
Rahoton ya ce filin da ake magana kai yana 'Kwankwasiyya City' da aka ba kamfanin WAECO a mulkin Sanata Rabi'u Kwankwaso.
Sai dai daga bisani tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kwace filin kan wasu dalilai.
Hukumar yaki da cin hanci ta yi bincike
A shekarar 2017, hukumar yaki da cin hanci ta yi bincike inda ta gano tsohon gwamnan da dan uwansa sune daraktocin kamfanin.
Hukumar daga bisani ta ba da shawara a kwace filin inda ta ce a lokacin kamfanin ba shi da inganci saboda haka bai cancanci ba shi fili ba.
Har ila yau, Ganduje ya yanki wani yanki a filin ya ba 'Malam Kato Square' da sauran filin ga asalin masu shi da kuma iyalan Dantata.
Sai dai Gwamna Abba ya ki amincewa da kwace filin inda ya yanki hekta 100 ya ba kamfanin WAECO.
Bayan sauraran korafe-korafen, Mai Shari'a, Usman Na’abba ya dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 27 ga watan Nuwambar 2024.
Gwamnatin Abba ta biya basuka a Kano
Kun ji cewa ofishin kula da basussuka na jihar Kano ya bayyana adadin lamunin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta biya waɗanda ta gada.
Shugaban ofishin ya bayyana cewa gwamnatin ta biya basussukan da suka kai N63bn na cikin gida da na ƙasashen waje.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin Abba ba ta karɓo ko sisi da sunan bashi ba tun bayan hawanta kan mulki a shekarar 2023.
Asali: Legit.ng