'Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma 7, Sun Ƙona Buhunan Masara 50 a Jihar Neja

'Yan Bindiga Sun Hallaka Manoma 7, Sun Ƙona Buhunan Masara 50 a Jihar Neja

  • Ƴan bindiga sun yi wa manoma kwantan ɓauna, sun kashe mutum bakwai a kauyen Bangi da ke ƙaramar hukumar Mariga a jihar Neja
  • Maharan sun kuma ƙona buhanan masara 50 bayan kashe mutanen, lamarin ya jefa fargaba a zukatan mazaunan Mariga
  • Rundunar ƴan sanda ta ce dakarunta da sojoji sun isa yankin donin daƙile faruwar haka a gaba da kuma ba manona kariya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Neja - Ƴan bindiga sun hallaka manoma aƙalla bakwai ciki har da ƴan banga kuma sun ƙona buhuna 50 na masara a jihar Neja.

Miyagun sun aikata wannan mummunan ta'adi ne a lokacin da suka mamayi manoman a Bangi, karamar hukumar Mariga da ke jihar a Arewa ta Tsakiya.

Muhammad Umaru Bago.
Yan bindiga sun kashe manoma bakwai a jihar Neja Hoto: Mohammed Umaru Bago
Asali: Twitter

Ƴan bindiga sun yiwa manoma kwantan ɓauna

Wasu majiyoyi sun shaidawa Daily Trust cewa mutanen sun tafi ɗauko masara daga gona bayan an yi girbi kwatsam ƴan bindigar suka mamaye su.

Kara karanta wannan

Mutane sun dauki doka a hannunsu, sun bankawa masu karbar kudin haraji wuta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun ce ƴan ta'addan sun kashe dukkan waɗanda ke cikin motar, sannan suka bankawa wa motar wuta.

Ɗaya daga cikin majiyoyin ta ce:

"‘Yan bindiga sun kashe manoma bakwai daga cikin manoman mu da suka je gona don kawo masarar da suka girbe gida.
"A farko laɓewa suka yi har sai da manoman suka loda masarar a kan mota, sannan suka buɗe masu wuta, bayan kashe su sai suka ƙona motar tare da masara buhu 50 a ciki."

Ya ce a yanzu abu ne mai wahalar gaske manoma a yankin Mariga su iya girbi amfanin gonarsu saboda fargabar kashe-kashe da satar mutanen da ƴan fashin daji ke yi.

Ƴan sanda da sojoji sun kai ɗauki yankin

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da kashe manoman guda bakwai.

Daily Post ta ruwaito Abiodun na cewa:

"Ranar 16 ga watan Nuwamba, da misalin karfe 3 na rana, wasu ƴan bindiga suka yi wa ƴan banga kwantan bauna a Makogi/Ungwan Elbi, suka kashe wasu daga cikinsu."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace ƴan uwan ɗan jarida ana tsaka da jimamin rasuwar mahaifiyarsa

Abiodun ya ce jami’an tsaron hadin gwiwa da suka hada da ‘yan sanda da sojoji sun isa yankin domin daƙile faruwar irin haka daba manoma kariya su girbe amfanin gonakinsu.

Ƴan bindiga sun kashe manoma

A wani labarin, an ji cewa ƴan ta'adda sun yi ta'addanci a jihar Neja bayan sun kai wani hari kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.

Ana zargin cewa tsagerun sun hallaka mutane takwas ciki har da wasu mata guda biyu da suka ƙi yarda su yi lalata da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262