Gobara Ta Lakume Azuzuwa a Niger, an Zargi Mashaya Tabar ‘Wiwi’ da Sanadinta
- Bayan gobara ta kama a wata makaranta da ke birnin Minna a jihar Niger, wasu mazuna yankin sun zargin mashaya tabar 'wiwi'
- Gobarar ta kama ne a daren ranar Alhamis 21 ga watan Nuwambar 2024 a makarantar Limawa da ke jihar
- Shugaban makarantar, Datti Dauda ya bayyana yadda ya samu labarin gobarar da kuma taimakon hukumar kashe gobara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Niger - Wasu azuzuwa sun kama da wuta a makarantar Limawa da ke birnin Minna a jihar Niger.
Ana zargin lamarin ya faru a daren ranar Alhamis 21 ga watan Nuwambar 2024 sanadin wasu mashaya tabar 'wiwi'.
Gobara ta lakume makarantar sakandare a Niger
Wasu mazauna yankin sun tabbatar da zarginsu cewa masu shan tabar ce sanadin gobarar saboda sakacinsu, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mai suna Ibrahim Mohammed ya ce masu shaye-shayen suna zuwa wurin domin gudanar da bushe-bushensu.
"Wadannan yara kullum suna zuwa domin shan taba kuma a wannan yanayi na hunturu komai kamawa da wuta yake yi."
"A daren jiya sun yasar da guntuwar tabar wacce ta yi sanadin tashin gobarar wanda sakacinsu ne ya jawo."
"Wata rana mun zo wani shiri mun gan su suna shaye-shaye, da muka tashi tafiya mun kaurace musu saboda gudun fitina, tabbas su ne sanadin tashin wutar saboda sakacinsu."
- Ibrahim Mohammed
Shugaban makarantar ya magantu kan gobarar
Shugaban makarantar, Datti Dauda ya ce ya samu labarin tashin gobarar ce bayan wani ya sanar da shi labarin iftila'in da ta afku.
Datti ya ce ya yi gaggawar kiran hukumar kashe gobara inda suka yi nasarar kawo karshenta, Punch ta ruwaito.
Gobara ta ci kasuwa a Plateau
Kun ji cewa rahotanni sun bayyana cewa mummunar gobara ta tashi a kasuwar Laranto da ke Jos ta Arewa, jihar Filato.
Shugaban kasuwar, Alhaji Idris Shehu, ya ce gobarar da ta tashi bayan an rufe kasuwar ta jawo asarar dukiyar miliyoyin Naira.
Sai dai shugaban sashen 'yan katako na kasuwar ya koka kan yadda 'yan kwana kwanan yankin suka ki kai masu dauki.
Asali: Legit.ng