'Abin da Ya Dace Ka Yi a Liyafar': Sheikh Dutsen Tanshi Ya Tabo Kabiru Gombe
- Yayin da ake ce-ce-ku-ce kan halartar liyafar daurin auren yar Sanata Rabiu Kwankwaso, Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya yi magana
- Sheikh Idris ya ce kwata-kwata bai dace malamai su halarci irin wannan wuri ba saboda cakuduwan maza da mata wanda haram ne
- Malamin ya shawarci Kabiru Gombe kan abin ya kamata ya yi kawai a wurin liyafar inda ya ce ya tashi ya fadakar ya tafi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi - Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi ya yi magana kan halartar liyafa da Sheikh Kabiru Gombe ya yi.
Dutsen Tanshi ya ce abin takaici ne yadda malamai da ake ganin girmansu za su halarci irin wannan wuri da ake tafka barna.
Sheikh Dutsen Tanshi ya shawarci Kabiru Gombe
Sheikh Idris ya fadi haka ne a cikin wani faifan bidiyon hudubar Juma'a da shafin Dutsen Tanshi Majlis Bauchi ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya fadawa Sheikh Kabiru Gombe abin da ya kamata ya yi a matsayinsa na mai fadakarwa domin kawo gyara a lamarin.
"Aka zo aka yi rawa aka yi kida aka yi cakuduwan maza da mata kuma aka samu malamai a wurin, kuma har malamin ya ce amaryar ta yi shiga na kamala."
- Sheikh Dutsen Tanshi
Liyafa: Sheikh Idris ya soki Kabiru Gombe
"Abin tambaya a nan, muzo kan hijabi da ke da sharuda guda takwas, shigar da ta yi akwai kamala a ciki? amma har a samu malami ya ce wai shigar kamala ce har yana kira a yi koyi da ita."
"Malam ka ji tsoron Alla, malama ka ji tsoron Allah, abin da ya dace ka yi sai ka tashi ka ce yan uwa Musulmi cakuduwan maza da mata haramun ne ka da ku sake sai ka sake cewa kade-kade haramun ne kada ku sake yi."
"Ka ce almubazzaranci da kudi a yanayin da wasu ba su samun abin da za su ci a rana ko kudin bude kai sai kace haramun ne a shari'ar Musulunci."
- Sheikh Idris Dutsen Tanshi
Cc-ce-ku-ce kan zuwan Kabiru Gombe liyafa
Kun ji cewa yan Najeriya da dama sun yi martani da aka gano wasu malaman Musulunci a wurin bikin 'dinner' na auren yar Rabiu Kwankwaso.
Hakan ya tayar da kura inda wasu ke ganin bai kamata malamai da suke kushe lamarin ba kuma za a gansu a wurin.
Asali: Legit.ng