Dalilin da Ya Sa Manufofin Shugaba Tinubu Suka Kawo Wahala da Tsadar Rayuwa a Najeriya

Dalilin da Ya Sa Manufofin Shugaba Tinubu Suka Kawo Wahala da Tsadar Rayuwa a Najeriya

  • Wale Edun ya bayyana cewa gwamnatocin da suka gabata ne suka jawo walaha da tsadar rayuwar da ake ciki a Najeriya
  • Ministan kudi da harkokin tattalin arziki ya ce duk da manufofin Tinubu na da radadi amma an ga canji a watanni 18 da hawan wannan gwamnatin
  • Ya ce kamata ya yi gwamnatocin baya su ɗauki matakan da Tinubu ya ɗauka amma ba su yi ba shiyasa ake shan wahala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ministan kudi da harkokin tattalin Arziki, Wale Edun, ya bayyana dalilin da ya sa manufofin shugaban kasa, Bola Tinubu suka kawo wahala a Najeriya.

Edun ya ce tsare-tsaren tattalin arzikin Tinubu sun haifar da walaha, kunci da tsadar rayuwa ne saboda gwamnatocin da suka gabata ba su ɗauki matakin da ya dace ba.

Kara karanta wannan

'Akwai yunwa': Tinubu ya magantu daga Brazil, ya ba yan kasa satar amsar shirinsa

Wale Edun da Tinubu.
Wale Edun ya bayyana abin da ya kawo yunwa da talauci a mulkin Tinubu Hoto: Wale Edun
Asali: Twitter

Ministan ya faɗi haka ne a wurin taron kaddamar da wani sababbin tsare-tsare na ma'aikata a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya (HCSF), Misis Didi Walson-Jack ce ta shirya taron a wani bangare na bikin cika kwanaki 100 da da naɗinta.

Manufofin Tinubu da suka kawo wahala

Idan baku manta ba a wurin bikin rantsuwa, Shugaba Tinubu ya sanar da tuge tallafin man fetur, lamarin da ya jawo tsadar mai daga N195 har ya kai N1,100.

Wannan mataki da ma wasu manufofin da Tinubu ya zo da su sun haifar da hauhawar farashin abinci da tsadar kayayyakin amfani na yau da kullum.

Dalilin shiga kunci a mulkin Tinubu

Sai dai Wale Edun ya ce rashin aiwatar da waɗannan tsare-tsare tun a gwamnatocin baya na ɗaya daga cikin abubuwan da suka jefa jama'a cikin ƙunci, The Sun ta rahoto.

"Kowa yana kallo bayan watanni 18 da aiwatar da tsare-tsaren tattalin arziki na mai girma shugaban kasa, an samu canji duk da ana cikin wahala."

Kara karanta wannan

Abin da Bola Tinubu ke yi don kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya a Najeriya

"Eh tabbas mutane na cikin wahala, ƙunci da tsadar rayuwa amma nasara da jin daɗi na nan tafe."

- Wale Edun.

Tinubu na ƙoƙarin sasanta manoma da makiyaya

A wani labarin, kun ji cewa Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta maida hankali wajen jawo masu zuba jari a ɓangaren kiwo domin magance rikicin manoma da makiyaya.

Shugaban ƙasar ya faɗi hakan a wurin ratttaɓa hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin sarrafa nama a ƙasar Brazil.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262