Gwamna Ya Zargi Magabacinsa da Sace Motoci 200 a Gidan Gwamnati, An Gano Wasu

Gwamna Ya Zargi Magabacinsa da Sace Motoci 200 a Gidan Gwamnati, An Gano Wasu

  • Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya kafa kwamiti na musamman domin kwato wasu motoci 200 da suka bace a jihar
  • Gwamna Okpebholo na zargin tsohon gwamnan jihar, Godwin Obaseki da mukarrabansa da kwashe motocin gwamnati
  • Daga bisani, an fitar da wata sanarwa da ke nuna an samu motocin guda uku daya tana cike da kayan tallafin abinci domin jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Gwamanan jihar Edo, Monday Okpebholo ya yi korafi kan batan motoci guda 200 bayan gwamnatin Godwin Obaseki ta tattare.

Gwamnatin jihar ta kafa kwamiti mai dauke da mambobi 12 domin kokarin kwato motocin da ake zargin Obaseki ya kwashe.

Gwamna ya zargi sace motoci 200 daga gidan gwamnati
Gwamna Monday Okpebholo ya zargi tsohon gwamna da sace motoci 200 a gidan gwamnati. Hoto: Governor Godwin Obaseki, Senator Monday Okpebholo.
Asali: Facebook

Gwamna Okpebholo ya zargi Obaseki da sace motoci

Channels TV ta ce Gwamna Monday Okpebholo ya bukaci Kelly Okungbowa ya jagoranci kwamitin domin kwato motocin.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta raba gardama a shari'ar Tinubu da gwamnoni 36 kan rarar kudi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Okpebholo ya ba kwamitin wa'adin makwanni biyu inda ya ce su tabbatar sun yi nasarar kwato motocin a hannunsu.

Okungbowa ya ce bayan awanni 24 an yi nasarar kwato guda uku daga cikin motocin da ake zargin Obaseki da hadiminsa sun kwashe.

Kayan da aka samu daga cikin motocin

Daga cikin motocin akwai bas da aka kwace makare da kayan tallafin abinci da aka ware domin rabawa al'ummar jihar Edo.

Kayan da ke cikin motar sun hada da buhunan shinkafa da gari wanda gwamnati ta ware domin al'umma, cewar rahoton Sahara Reporters.

Sanarwar ta bukaci hadin kai daga al'umma domin samun bayanai wanda ya yi sanadin kwato wasu motocin tun farko.

Gwamna Okpebholo ya ce an rasa inda Obaseki yake

Kun ji cewa sabon gwamna a jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo ya yi zargin cewa ana neman Gwamna Godwin Obaseki an rasa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ba da umarnin rufe makarantu saboda mutuwar Sanata, bayanai sun fito

Okpebholo ya ce tun ranar Juma'a 8 ga watan Nuwambar 2024 har zuwa yau ba a san inda Obaseki yake ba Hakan ya biyo bayan zargin da.

Wannan na zuwa ne bayan Obaseki ya yi zargin cewa Okpebholo bai gayyace shi zuwa taron rantsar da shi ba a ranar 12 ga watan Nuwambar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.