Zanga Zanga: Gwamnan Kano Ya Ba Matasan da Aka Tsare Aikin Yi bayan Sun Fito
- Gwamnatin Kano ta bayar da takardar daukar aiki ga matasa biyu da su ka yi zanga zangar adawa da yunwa bayan karbo su
- A ranar Alhamis ne gwamnati ta mika yaran ga iyayensu bayan an kammala duba lafiyar jikinsu da ta kwakwalwa
- Sauran yaran kuma sun samu tagomashin komawa karatu da kuma kyautar N50,000 domin amfanin ya da gobe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta Kano ta taimaki rayuwar wasu daga cikin matasan da aka tuhuma da cin amanar kasa a lokacin zanga zanga.
Gwamnatin jihar ta dauki matakin taimakon wasu matasa biyu daga cikin mutane 76 da mataimakin shugaban kasa, Kashim Stettima ya mika mata.
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa a ranar Alhamis ne gwamnatin Kano ta mika yaran ga iyayensu, tare da ba wa matasa biyu daga cikinsu takardar daukarsu aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano ta ba matasa aiki
Jaridar New Telegraph ya wallafa cewa an dauki matasa guda biyu aiki bayan damka su ga iyayensu a asibitin Muammadu Buhari dake Giginyu.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan bayar da aikin yi, gwamnati ta kuma mayar da wasu daga cikin matasan zuwa makaranta domin kara inganta rayuwarsu.
An tallafawa yaran Kano da aka cafke
Daga cikin wasu abubuwan da matasan su ka samu akwai tallafin N50,000 da gidauniyar ta Bafarawa ta raba ga dukkanin matasan 12 da su ka shaki iskar yanci.
Wakilin iyayen yaran, Nura Ahmad Muhammed ya yaba da kokarin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf da sauran kungiyoyi su ka yi wajen ceto yara.
An mika yaran Kano ga iyayensu
A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kammala binciken lafiyar yaranta da aka karbo daga hannun gwamnatin Bola Tinubu da ke zarginsu da cin amanar kasa.
Kwamishinan lafiya na Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya jagoranci mika yaran ga iyayensu, inda ya ja masu kunnen da su guji shiga duk wata fitina da ta taso a cikin kasar.
Asali: Legit.ng