Kotun Koli Ta Raba Gardama a Shari'ar Tinubu da Gwamnoni 36 kan Rarar Kudi
- Yayin da gwamnoni 36 suka shigar da korafi kan Gwamnatin Tarayya, Kotun Koli ta yanke hukunci kan lamarin
- Kotun da ke zamanta a birnin Abuja ta yi fatali da korafin da gwamnoni suka shigar kan cewa ba shi da tushe bare makama
- Hakan na zuwa ne yayin da gwamnonin suke neman Gwamnatin Tarayya ta yi bayani kan kudin gas da sauran albarkatun mai tun daga 1999
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun Koli ta yi zama kan shari'ar da gwamnoni 36 suka shigar da Gwamnatin Tarayya.
Kotun ta yi fatali da korafin gwamnonin domin tilasta gwamnatin bayanin kudin gas tun daga shekarar 1999 zuwa yau.
Kotu ta yi hukunci a shari'ar Tinubu, gwamnoni
Channels TV ta ruwaito cewa kwamiti mai alkalai bakwai ne ya yi hukuncin a yau Juma'a 22 ga watan Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta ce korafin da aka shigar ba shi da inganci wanda Ministan shari'a, Lateef Fagbemi ke kare Gwmanatin Tarayya.
Tun farko, gwamnonin sun nemi bahasi kan kudin gas da riba ko rarar da aka samu a bangaren mai tun daga shekarar 1999.
Dalilin fatali da korafin gwamnoni kan Tinubu
Mai Shari'a, Mohammed Lawal Garba ya ce an riga an yi hukunci kan korafin a zaman kotun tun a can baya, cewar The Nation.
Lawal Garba ya ce masu korafi suna neman sake tayar da maganar ce da Kotun Koli ta kawo karshenta a shari'ar kwamishinan shari'a na Bauchi da Ministan shari'a.
Sauran alkalan da ke cikin kwamitin sun hada da Abba-Aji da Emmanuel Agim da Simon Tsammani da Stephen Adah da Jamilu Tukur inda suka goyi bayan hukuncin.
Kotun Koli ta yi hukunci kan kananan hukumomi
Kun ji cewa Kotun Koli da ke Abuja ta sake ba da umarni bayan hukuncin da ta yi kan 'yancin kananan hukumomi a Najeriya bayan korafin.
Gwamnatin Tarayya Kotun ta umarci ba kansiloli da shugabannin kananan hukumomi a Najeriya wa'adin shekaru hudu kamar yadda gwamnonin jihohi ke yi.
Wannan na zuwa ne bayan hukuncin da kotun ta yi kan ba kananan hukumomin 'yancinsu yayin da gwamnonin jihohi ke dakile su.
Asali: Legit.ng