Yadda gwamnati ta rage wa masu kudi kudin gas ana dab da zabe

Yadda gwamnati ta rage wa masu kudi kudin gas ana dab da zabe

- Hukumar kididdiga ta kasa tace farashin gas na girki ya sauka a watan Junairu

- Jihar Adamawa da Cross river suna daga jikin jihohin da farashin su yafi na kowacce jiha

- Osun,Ogun da jihar Enugu sunfi kowacce jiha saukin farashi

Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa
Zaben 2019 na Najeriya na ta matsowa
Asali: UGC

Hukumar kididdiga ta kasa ta bayyana cewa farashin gas din girki mai girman 5kg ya sauka daga N2,052.72 a watan Disemba shekara ta 2018 inda ya koma 2,039.82 a watan Junairu.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafin ta na yanar gizo a ranar Juma'a.

Inda tace farashin cika silindar gas ta girki ya sauka da kaso -0.63% a rahoton ta na wata- wata yayin daya sauka da -6.86% a rahoton shekara-shekara.

GA WANNAN: Matasan Yarabawa sunce bassu tare da kungiyar dattijansu ta Afenifere masu son Atiku

Hukumar ta bayyana jihohin da sukafi kowacce jiha tsadar gas din,jihar Bauchi suna cika silindar gas me nauyin 5kg a N2,540.00 yayin da jihar Adamawa da Cross river suke cikata N2,350.00 sai jihar Borno suna cikata akan N2,325.00.

Yayin da a daya bangaren kuma ta fitar da jihohin da sukafi kowacce jiha saukin farashin gas din wanda ya hada da jihar Ogun,Enugu da Osun.

Bangaren Diesel kuma ya haura da N225.09 a cikin watan Junairu inda ya haure farashin sa na watan Disemba shekara ta 2018.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaran.@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng