REA: EFCC Ta Dura Kan Babban Jami'in Gwamnati, Ana Zargin Ya Wawure N223m
- EFCC ta gurfanar da daraktan kula da harkokin ma’aikata a hukumar raya wutar lantarki ta karkakara (REA), Sulaiman Bulkwang
- Huakumar na tuhumar Bulkwang da laifin safarar kudaden haram da kuma wawure wasu kdaden da suka kai N223,412,909
- Bulkwang ya musanta dukkanin tuhume-tuhumen da ake yi masa yayin da kotu ta ba da ajiyarsa a gidan yari zuwa 3 ga Fabrairu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar EFCC ta gurfanar da Sulaiman Garba Bulkwang, daraktan harkokin ma’aikata na hukumar wutar lantarki ta karkara (REA), a gaban kotu.
An gurfanar da Bulkwang a gaban Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta babbar kotun tarayya, Abuja, kan tuhume-tuhume biyar na safara da karkatar da kuɗi.
EFCC ta maka jami'in gwamnati a kotu
Ana zargin Bulkwang da karkatar da kuɗaɗen da suka kai N223,412,909 waɗanda aka ware don ayyukan kamfanonin tuntuba a hukumar REA, inji rahoton FRCN.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tuhumar farko ta ce Bulkwang ya umurci shugaban kamfanonin Cees Assist Resources da Brainstask Value Resources da ya tura masa N138,123,969.
Wadannan kudin da ya umarci shugaban kamfanonin ya tura masa na daga cikin N279,330,000.00 da REA ta biya ga kamfanonin a matsayin kudin kwangilarsu.
Ana zargin jami'in ya karkatar da N45m
A tuhuma ta biyu, EFCC ta zargi Bulkwang da karkatar da N45,000,000.00, wani bangare na kudaden da aka tara ga asusun bankunan wasu kamfanoni.
Kamfanonin su ne: Dammy Gold Program Ltd, World Class Business, Green Haven da De-Sam Rose – Base Ltd, kuma REA ce ta biya kudin matsayin kudin kwangilar kamfanonin.
Hukumar EFCC ta ce wadannan laifuffuka da ake zargin daraktan ya aika sun ci karo da tanade-tanaden dokar hana safarar kuɗi ta shekarar 2022.
An iza keyar Bulkwang zuwa gidan yari
Bayan an karanto masa tuhume-tuhumen, Bulkwang ya musanta su yayin da lauyansa bai samu damar halartar zaman kotun ba.
Lauyan EFCC, Ekele Iheanacho, SAN, ya nemi kotu ta ɗage shari’ar tare da umarnin tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali.
Mai Shari’a Abdulmalik ta ɗage zaman shari’ar zuwa ranar 3 ga Fabrairu, 2024, domin sauraron buƙatar belin wanda ake tuhuma.
Kotun ta bayar da umarnin tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa ranar da koma za ta yi zama na gaba.
Tinubu ya dakatar da shugaban REA
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Ahmad Salihijo Ahmad daga mukamin shugaban hukumar REA tare da manyan daractoci kan almundahana.
Shugaban ƙasar ya naɗa waɗanda zasu maye gurbinsu kuma daga cikin wadanda aka nada akwaiɗan shugaban APC, Abdullahi Ganduje, wanda aka ba mukamin darakta.
Asali: Legit.ng