'Korar Musulmi a Gwamnatin Muslim Muslim,' Sheikh Jingir Ya Jefo Zargi

'Korar Musulmi a Gwamnatin Muslim Muslim,' Sheikh Jingir Ya Jefo Zargi

  • Shugaban kungiyar Izala mai hedikwata a Jos ya yi magana kan yadda ake sukansa a kan gwamnatin Muslim Muslim a Najeriya
  • Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir ya ce ana samun masu sukar Muslim Muslim kuma suna shiga gwamnatin Bola Tinubu
  • Malamin ya yi zargin cewa akwai wadanda suke shiga gwamnatin Muslim Muslim kuma suna korar Musulmai a wuraren aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi magana kan masu sukansa a kan gwamnatin Bola Tinubu.

Malamin ya ce har yanzu ba shi da wani abu da ya fi masa Musulunci kuma zai cigaba da goyon bayan Muslim Muslim.

Sheikh Jingir
Sheikh Jingir ya yi magana kan masu sukar Muslim Muslim suna shiga gwamnati. Hoto: Bayo Onanuga|Hamza Muhammad Sani
Asali: Facebook

Sheikh Jingir ya yi maganar ne kafin sallar Juma'a a Abuja kamar yadda shafin masallacin Guzape ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Rundunar Hisbah ta ƙara faɗaɗuwa a Arewa, ana neman ba su cikakken iko

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jingir vs masu sukan Muslim Muslim

Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir ya ce duk da suka da ake masa a kan Muslim Muslim har yau ba shi da tabo.

Malamin ya ce akwai wadanda suka yi kira a zabi Kirista da Kirista amma babu wanda yake sukansu a kasar nan.

Shehin malamin ya yi zargin cewa wasu da suka soki Muslim Muslim yanzu sun shigo gwamnati suna korar Musulmai.

"Ku da kuke zagin Muslim Muslim me yasa da Allah ya ba mu kuke zuwa kuna tare mana wuri kuna kora mana Musulmi?
Kai da kake zagin Muslim Muslim an dauko ka da kazantarka an baka babban matsayi kuma kana korar Musulmi.
Allah yasa ma'aikatar bincike ta lelleka ta gano waye mai kora mana Musulmai a ofis.".

- Sheikh Jingir

Sheikh Jingir ya yi addu'ar Allah ya karawa dukkan shugabannin Najeriya lafiya ya kuma ba su ikon yin daidai.

Kara karanta wannan

'Muna goyon bayanka': Malamin Musulunci ya magantu da Abba Hikima ya maka Wike a kotu

A karshe, malamin ya ce idan Bola Tinubu na tafiya a yanzu za a dauka saurayi ne duk da a baya ana cewa ba shi da cikakkiyar lafiya.

An titsiye mai sukan Muslim Muslim

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon hadimin Atiku Abubakar da ya shiga gwamnatin Bola Tinubu ya yi hira da yan jarida bayan shugaban kasa ya ba shi muƙami.

Daniel Bwala ya shahara da sukan tikitin Muslim Muslim a kafafen sadarwa a lokacin yakin neman zaben shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng