'Karshen Turji da Yan Bindiga Ya Kusa': Ministan Tsaro bayan Karbar Jirage daga Turkiyya

'Karshen Turji da Yan Bindiga Ya Kusa': Ministan Tsaro bayan Karbar Jirage daga Turkiyya

  • Ministan tsaro a Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya bukaci hadin kan sojoji game da yaki da yan ta'adda
  • Badaru ya bayyana cewa saura kiris kwanakin yan ta'adda da masu garkuwa da mutane ya kare a fadin kasar baki daya
  • Hakan na zuwa ne yayin kaddamar da jiragen yaki masu saukar ungulu na T129 ATAK a jihar Katsina domin fatattakar yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Ministan tsaro, Badaru Abubakar ya sha alwashin kawo karshen yan ta'adda a Najeriya.

Badaru ya ce karshen yan ta'adda da masu garkuwa da mutane ya zo kusa duba da jiragen yaki da suka karba daga Turkiyya.

Badaru ya sha alwashin kawo karshen yan ta'adda
Ministan tsaro, Badaru Abubakar ya ce saura kiris su kawo karshen yan ta'adda. Hoto: Nigerian Air Force HQ.
Asali: Facebook

Badaru ya roki sojoji kan yaki da ta'addanci

Ministan ya bayyana haka ne a jihar Katsina yayin kaddamar da jiragen yaki masu saukar ungulu, kamar yadda rundunar tsaro ta wallafa a shafinta.

Kara karanta wannan

'Akwai yunwa': Tinubu ya magantu daga Brazil, ya ba yan kasa satar amsar shirinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Badaru ya bayyana irin kayan yaki na jiragen sama masu saukar ungulu na T129 ATAK da suka saya daga kasar Turkiyya.

Tsohon gwamnan ya bukaci sojojin Najeriya da kara kaimi wurin tabbatar da kawo karshen makiyan kasar.

“Karshen ayyukan ‘yan ta’adda da ‘yan daba masu dauke da makamai a kasar ya kusa."

- Mohammed Badaru Abubakar

An kara samun karfi kan yaki da ta'addanci

Ministan ya ce karin jirage guda biyu da aka kawo a watan Satumbar 2024 sun karfafa yaki da yan bindiga, cewar TRT Afirka.

Wannan na zuwa ne yayin da yan ta'adda ke cigaba da addabar yankunan Arewacin Najeriya.

A yan kwanakin nan, sojoji sun yi ta bata-kashi da yan ta'adda karkashin kasurgumi Bello Turji.

Mukaddashin hafsan sojoji ya gargadi Turji

A wani labarin, kun ji cewa sabon mukaddashin hafsan sojoji a Najeriya, Laftanar-janar Olufemi Oluyede ya sha alwashin kakkabe yan ta'adda gaba daya.

Kara karanta wannan

"Babu Lakurawa a Najeriya," Sanata ya fadi inda aka kora yan ta'adda

Laftanar-janar Olufemi ya bukaci yan ta'adda su shirya domin a wannan lokaci ba za su ji ta dadi ba ko kadan karkashin ikonsa.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan bikin binne marigayi tsohon haifsan sojoji, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.