'Yan Majalisa ba Su Dandara ba, Za Su Sake Jajubo Kudurin Kara Wa'adin Masu Mulki

'Yan Majalisa ba Su Dandara ba, Za Su Sake Jajubo Kudurin Kara Wa'adin Masu Mulki

  • Wasu yan majalisar wakilai 34 sun ja daga kan sake dawo da kudurin kara wa'adin mulki a Najeriya zuwa shekaru shida
  • A ranar Alhamis ne yan majalisar su ka yi watsi da kudurin, wanda ya kunshi wadansu tsare-tsare kan mulkin kasa
  • Amma wanda ya jagoranci gabatar da kudurin, Hon. Ikenga Ugochinyere ya bayyana cewa ba za su karaya da matakin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja Yan majalisa da su ka bijiro da kudurin kara shekarun mulkin shugaban kasa, gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi sun kafe kan bakatarsu.

A ranar Alhamis ne majalisar wakilan Najeriya ta yi watsi da dokar da ke neman a rage wa’adin mulkin shugabannin zuwa guda daya na shekaru shida.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba, ana zargin harin sojoji kan yan ta'adda ya hallaka bayin Allah

Majalisa
Ana shirin sake bijiro da kudurin kara wa'adin mulkin shugaban kasa Hoto: House of Representatives
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta bayyana cewa yan majalisar su 34 sun ce ba za su karaya da rashin nasarar kudurin a wannan lokaci ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa za ta nemi karin wa’adin mulki

PM News ta ruwaito dan majalisar Imo, Hon. Ikenga Ugochinyere ya jagoranci kudurin karin wa’adin mulki ya ce su na shirin sake bijiro da bukatarsu a gaban majalisa.

Baya ga batun karin shekarun mulki, kudurin ya kunshi bukatar daidata karba-karba tsakanin shiyyoyi kan zaben shugaban kasa da kara ofishin mataimakin shugaban kasa.

Yan majalisa na son a kara wa’adin mulki

Hon. Ikenga Ugochinyere ya bayyana fatan takwarorinsa a majalisa za su ga amfanin kudurin kara wa’adin mulkin shugaban kasa a nan gaba kadan.

Hon. Ugochinyere ya ce;

“Matakin da majalisa ta dauka a jiya (Alhamis) na kin amincewa da wa’adin mulki daya na shekaru shida ga duk zababbun shugabanni ba zai karya mana gwiwa ba."

Kara karanta wannan

Kwankwaso da wasu manyan Arewa da suka nuna adawa da kudirin harajin Tinubu

Ya jaddada cewa za sake zama domin duba kudurin tare da dawo da shi gaban majalisa yadda za a gamsu da abubuwan da zai kunsa.

Majalisa ta ki amincewa da kara shekarun mulki

A baya mun ruwaito cewa majalisar wakilan Najeriya ta yi fatali da kudurin da aka bijiro gabanta na kara wa'adin mulkin zababbun shugabanni zuwa shekaru shida a kasar nan.

A zaman da ta yi a ranar Alhamis, shugaban majalisa ya nemi ra'ayin wakilan na barin kudurin ya kai matakin karatu na biyu, amma akarinsu su ka ki amincewa da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.