Malaman Izalah Sun Ziyarci Sanata Barau, Sun Jero Ayyukan Alheri da Yake Yi a Kasa
- Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yi godiya bayan ziyarar malaman Izalah a ofishinsa
- Sanatan ya nuna jin dadinsa da Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatul Sunnah (JIBWIS) reshen Kano ta Arewa ta kai masa ziyara
- Hakan ya biyo bayan ziyarar da malaman suka kai domin nuna goyon baya ga sanatan kan irin ayyukan da yake yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ƙungiyar Izalah a mazabar Kano ta Arewa ta kai ziyara ofishin Sanata Jibrin Barau a Abuja.
Gamayyar malaman sun ziyarci mataimakin shugaban Majalisar Dattawa ne karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Usman Bichi.
Malaman Izalah sun yabawa Sanata Barau Jibrin
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Barau shi ya tabbatar da haka a yau Juma'a 22 ga watan Nuwambar 2024 a shafinsa na X.
Malaman sun yabawa Sanata Barau kan irin ayyuka da yake yi da ya shafi al'ummar yankin gaba daya.
Musamman malaman suka yaba kan gudunmawarsa a ɓangarorin lafiya da ilimi da hanyoyi da kuma tallafawa al'umma.
Sanata Jibrin ya godewa malaman Izalah
"Na karbi bakuncin malamai karkashin kungiyar Jama'atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatul Sunnah (JIBWIS) a Kano ta Arewa a Majalisar Tarayya da ke Abuja a yammacin Alhamis."
"Sheikh Muhammad Usman Ahmed Bichi wanda ya jagoranci tawagar ya yaba min kan irin gudunmawa da na bayar a bangarori da dama."
"Yayin da suke nuna goyon baya a gare ni, sun yi addu'ar Ubangiji ya ba ni lafiya da kariya da taimako domin cigaba da shawo kan matsalolinsu."
"Ina matukar yi musu godiya kan wannan ziyara da ba su tabbacin cigaba da inganta rayuwar al'umma."
- Barau Jibrin
Kano: Sanata Barau ya sake gigita NNPP
Kun ji cewa jam'iyyar NNPP ta sake gamuwa da matsala yayin da wasu 'yan takarar kansila suka sauya sheka zuwa APC a jihar Kano.
Karkashin jagorancin Jamilu Isyaku Getso, 'yan takarar sun sanar da komawarsu APC ne ta hannun Sanata Barau Jibrin.
Yan takarar sun shaidawa Barau cewa sun sauya shekar ne saboda rashin adalcin da shugabannin NNPP suka yi musu.
Asali: Legit.ng