Yan Ta'adda Sun Ƙara Lalata Turken Lantarki, Sun Sace Kayayyaki
- Kamfanin rarraba wuta na kasa (TCN) ya tabbatar da cewa wasu yan ta'adda sun kai hari kan wani turken wuta a Kudancin Najeriya
- Bayanan TCN sun nuna cewa miyagun sun kai hari kan turken wuta na Ahoada-Yenagoa 132kV kuma suka tafka sata a kan wasu layukan lantarki
- Kamfanin TCN ya yi kira ga al'ummar Najeriya kan bayar da gudummawa wajen lura da turakan wuta domin kare su daga sharrin miyagu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bayelsa - Yan ta'adda sun kawo cikas kan gyaran lantarki da ake a wasu sassan Kudancin Najeriya.
Rahotanni na nuni da cewa yan ta'adda sun kai hari kan layin wuta da ya harba lantarki Bayelsa tare da tafka sata.
Legit ta tattaro bayanan da TCN ya yi ne a cikin wani sako da kamfanin ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Jumu'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan ta'adda sun lalata turken lantarki
Kamfanin rarraba wuta na kada TCN ya ce wasu yan ta'adda sun lalata turken wuta na Ahoada-Yenagoa 132kV ana tsaka da gyarasa.
TCN ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a ranar 19 ga watan Nuwamba inda miyagun suka kai hari cikin dare.
Lamarin ya shafi layukan lantarki na 29 da 30 a yankin inda aka sace daya bisa uku na kayayyakin da ake gyara da su.
"Bincike da muka yi ya nuna cewa an kai hari wajen ne a cikin dare amma a yanzu haka mun dauki matakai.
Mun dauki wadanda za su ba da tsaro a yankin Ula Ikata na karamar hukumar Ahoada ta Yamma.
Waɗanda aka dauka za su cigaba da ba da tsaro a wajen har sai an kammala gyara kuma ana cigaba da maye kayayyakin da aka sace."
- Kanfanin TCN
Rahoton Vanguard ya nuna cewa TCN ta ce akwai buƙatar saka ido a kan turakan wuta da ake yawan lalatawa.
Haka zalika TCN ta yi kira ga jami'an tsaro da al'umma kan su rika gadin turakan wutar domin hana yan ta'adda lalata su.
TCN na fama da yan ta'adda wajen gyara
A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin rarraba wutar lantarki na kasa (TCN) ya shirya taro na musamman domin fito da wasu bayanai.
Shugaban TCN, Injiniya Sule Ahmed Abdulaziz ya bayyana yadda injiniyoyi suke fama da yan bindiga a wajen gyaran turakan wuta.
Asali: Legit.ng