ICPC Ta Fara Binciken Ayyukan Gwamnatin N41bn a Kananan Hukumomin Jihar Kano

ICPC Ta Fara Binciken Ayyukan Gwamnatin N41bn a Kananan Hukumomin Jihar Kano

  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta kaddamar da bincike kan wasu ayyuka da aka gudanar a fadin jihar
  • Binciken zai shafi wasu ayyuka 106 na mazabu da gwamnati da aka gudanar a kananan hukumomin Kano 44
  • Shugaban ICPC reshen jihar, Ibrahim A Garba ta cikin sanarwar da ya fitar a yammacin Alhamis ya ce kudin ayyukan sun kai N41bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta fara bibiyar wasu ayyukan mazabu da wadanda gwamnati su ka ce sun aiwatar.

Sanarwar da ICPC ta raba ga manema Labarai a Kano, daga ciki har da Legit ta ce za ta bibiyi ayyukan da adadinsu ya kai 106 a dukkanin kananan hukumomin Kano 44.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba, ana zargin harin sojoji kan yan ta'adda ya hallaka bayin Allah

Jihar Kano
ICPC ta fara binciken ayyukan gwamnati a Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin sanarwar da shugaban ICPC reshen Kano, Ibrahim A Garba, ya fitar a yammacin Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ICPC za ta binciki ayyuka a jihar Kano

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) reshen Kano ta ce za ta kawar da almundahana a cikin ayyukan mazabu da na gwamnati da aka aiwatar a jihar.

Shugaban ICPC, Ibrahim A Garba ne ya tabbatar da haka, inda ya ce sun tanadi kwararrun jami'ai domin binciken ayyukan da kudinsu ya kai N41bn.

Kano: Ayyukan da ICPC za ta bincika

ICPC ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike kan ingancin wasu daga cikin ayyukan da gwamnati ta aiwatar ne a bangaren da su ka fi shafar jama'a kai tsaye.

Ɓangarorin da ayyukan za su fi mayar da hankali akwai ilimi, lafiya, noma, samar da ruwan sha, harkar samar da lantarki, gina titunan karkara da cigaban matasa.

Kara karanta wannan

An samu rabuwar kai a APC kan zargin sakataren gwamnatin Tinubu da ƙabilanci

ICPC na binciken yan majalisar Kano

A wani labarin kun ji cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta kaddamar da binciken wasu daga cikin kusoshin majalisar dokokin jihar Kano bisa zargin badakala.

ICPC ta na tuhumar kakakin majalisar, mataimakin kakaki, shugaban masu rinjaye da magatakarda da masaniya a cikin badakalar kwangilar sayo magunguna a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.