"Babu Lakurawa a Najeriya," Sanata Ya Fadi Inda Aka Kora Yan Ta'adda
- Sanatan Kebbi, Adamu Aliero ya bayar da labari mai dadi kan ayyukan sojojin Najeriya wajen kakkabe Lakurawa da su ka kutso kasar
- Sanata Aliero, ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a ya tabbatar da cewa an yi nasarar fatattakar yan taaddan daga Najeriya
- Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta bayar da karin kayan aiki ga dakarun sojojinta domin tabbatar da kawo karshen kungiyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kebbi – Sanata mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya, Adamu Aliero ya bayar da tabbacin cewa dakarun kasar nan sun fatattaki yan ta’addan Lakurawa.
Sanata Aliero ya bayyana haka ne a ranar Juma’a ta ckin sanarwar da ya fitar a babban birnin tarayya Abuja kan cigaban da sojoji su ka samu a kan Lakurawa.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa cigaban na zuwa ne bayan Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya mika wasu manyan kayan aiki ga zaratan dakarun kasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kora Lakurawa wajen Najeriya
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Sanatan Kebbi ta Tsakiya, Adamu Aliero ya ce sojojin Najeriya sun yi nasarar fitar da yan ta’addan Lakurawa daga cikin Najeriya.
Ya bayyana cewa an samu tabbacin korar miyagun yan ta’addan, masu tsatstsauran ra’ayi zuwa makwabciyar kasar nan, jamhuriyyar Nijar.
“A kawo karshen Lakurawa,” Sanata
Sanatan Kebbi ya ce dakarun Najeriya sun kammala aikinsu na fatattakar yan ta’addan da su ka kunno kai, kuma ba za su iya ketare iyakar kasar nan ba.
Sanata Adamu Aliero ya kara da cewa;
“Dakarun mu ba za su iya haurawa iyakar kasa da kasa ba. Yanzu ya rage a yi amfani da alakar soji tsakaninmu da Nijar na kawo karshen ta’addanci su kammala aikin.”
An samu rahotannin Lakurawa sun tafka barna a Kebbi, wanda ya sa Sanata Aliero da wasu yan majalisa neman daukin Ministan tsaro.
Gwamnati ta dauki matakai kan Lakurawa
A wani labarin kun ji yadda gwamnatin Najeriya ta fara daukar mataki domin dakile tasirin kungiyar ta’addancin nan ta Lakurawa da ke kokarin kawo tarzoma a yankin Arewacin kasar.
Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta zuba idanu ta na kallon sabuwar kungiyar yan ta’addan ta cimma rugurguza zaman lafiya ba.
Asali: Legit.ng