An Shiga Fargaba, Ana Zargin Harin Sojoji kan Yan Ta'adda Ya Hallaka Bayin Allah

An Shiga Fargaba, Ana Zargin Harin Sojoji kan Yan Ta'adda Ya Hallaka Bayin Allah

  • Ana fargabar harin da sojoji su ka kai domin fatattakar yan ta'adda a Katsina ya salwantar da rayukan mutanen gari
  • An ruwaito cewa mutane da dama ne su ka kwanta dama, yayin da wasu da yawa su ka samu mugayen raunuka
  • Gwamnatin jihar ta yi karin bayani, inda ta ce sojojin kasar nan sun san yadda za su gudanar da aikinsu a cikin kwarewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina Harin da sojojin sama su ka kai domin fatattakar yan ta’adda a kauyen Shuwa da ke gundumar Ruwan Godiya a karamar hukumar Faskari a Katsina ya bar baya da kura.

A kokarin ganin an kawar da ta’addanci a yankin, wasu sun ce harin sojojin ya kashe mazauna yankin da ba su aikata laifin komai ga hukumomin tsaron kasar nan ba.

Kara karanta wannan

Hana jagoran Lakurawa aure ya jawo arangama, rayuka sun salwanta a Nijar

KATSINA
Gwamnatin Katsina ta ce ba a kashe kowa bisa kuskure ba Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Leadership ta wallafa cewa sojojin sun yi aman wuta ta sama a safiyar Alhamis, inda mazauna yankin su ka ce an kashe da yawa daga cikinsu bisa kuskure.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shiga damuwa bayan harin sojojin sama

An shiga damuwa kan ayyukan sojojin kasar nan na yaki da yan ta’adda bayan kisan mazauna kauyen Shuwa a kokarin kawar da miyagun yan bindiga.

Sahara Reporters ta wallafa cewa ana fargabar harin ya jikkata wasu da dama, wanda yanzu haka ke cikin mawuyaci hali.

Gwamnati ta yi karin haske kan harin da aka kai

Kwamishinan tsaron cikin gida na Katsina, Dr. Nasiru Mu’azu ya musanta harin da ake cewa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama bisa kuskure.

Dr. Nasiru Mu’azu ya ce;

“Duk wanda ya fada maku an kai hari bisa kuskure karya ya ke. An jefa bam ne kan yan ta’adda. Rundunar tsaron Najeriya ta na da kwarewa, kuma an kai harin ne bayan gudanar da bincike da tabbatar da bayanan sirri.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano na shirin cika alkawari, an fara runtumo gagarumin aiki a bangaren ilimi

An tura jiragen yaki ga sojoji a Katsina

A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Najeriya ta kaddamar da sababbin jiragen yaki a jihar Katsina a wani bangare na karafawa sojoji wajen fatattakar miyagun yan bindiga a Arewa.

Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ne ya jagoranci tawagar kaddamar da jiragen yakin samfurin ATAK-129 domin kakkabe yan bindigar da su ka hana yankin zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.