Katsina: Bankin Duniya Ya Ware Biliyoyi domin Gina Makarantu Kusan 100
- Bankin duniya ya dauko shirin bunkasa ilimi wajen samar da makarantu da kayan aiki ga dalibai da malamai a Najeriya
- A jihar Katsina, bankin ya ware biliyoyin kudi domin gida makarantu sakandare kusan 100 a ƙananan hukumomin daban daban
- Gwamna Dikko Umaru Radda ya yi na'am da shirin inda ya jagoranci kaddamar da rukunin farko na aikin a Kofar Kaura
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - Shirin Agile karkashin bankin duniya zai kashe biliyoyi wajen gina makarantu a jihar Katsina.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya yi jawabi yayin bude rukunin farko na aikin a makarantar Muhammadu Dodo a Kofar Kaura.
Hadimin gwamna Radda, Ibrahim Kaulaha Muhammad ya wallafa yadda aka bude makarantar a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a gina makarantu 75 a jihar Katsina
Shirin Agile na bankin duniya ya aza tubalin gina makarantun sakandare 75 a kananan hukumomin Katsina.
Ana sa ran cewa bayan gina makarantun za a yi horo na musamman ga malamai da samar da kayan aiki na zamani.
Shugaban Agile a jihar Katsina, Dr Mustapha Shehu ya ce bankin duniya ya ware sama da Naira biliyan 30 domin aikin.
"A a rukuni na biyu na shirin, za a fadada shi wajen ba da damar koyon sana'o'i da yi wa malamai horo."
- Dr Mustapha Shehu
Bayanin gwamna Radda kan aikin makarantu
Yayin da yake jawabi, gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa shirin zai taimaka wajen inganta ilimi a Katsina.
Gwamna Dikko Radda ya kara da cewa shirin ya dace da ƙoƙarin da suke wajen bunkasa ilimi a jihar.
"Za mu cigaba da samar da makarantu da yanayi mai kyau da za a koyar da al'ummar jihar Katsina.
Za mu tabbatar dukkan yan jihar Katsina sun samu ingantaccen ilimin da sauran damarmakin rayuwa."
- Dikko Umaru Radda
Radda ya yi ta'aziyyar hakimin Kurfi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa kan rasuwar Hakimin Kurfi, Alhaji Ahmadu Kurfi.
Malam Dikko Radda ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen ma'aikacin gwamnati wanda ya ba da gudunmawarsa ga Najeriya a ɓangarori daban-daban.
Asali: Legit.ng