'Za a Kore Shi daga Villa': Jagoran PDP Ya Hango Abin da Zai Faru da Tinubu a 2027
- Tsohon mataimakin shugaban PDP ya ce 'yan Najeriya na jiran zaben 2027 domin korar Shugaba Bola Tinubu daga Aso Villa
- Chief Bode George ya nuna damuwarsa kan rarrabuwar kawuna a cikin PDP inda ya nemi a gyara matsalar kafin zaben 2027
- Ya ƙara da cewa akwai buƙatar PDP ta dinke barakarta domin ceto Najeriya daga cikin mawuyacin halin da APC ta jefa ta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Cif Bode George, tsohon mataimakin shugaban PDP, ya ce 'yan Najeriya za su kori gwamnatin APC karkashin Shugaba Bola Tinubu daga Aso Rock a zaben 2027.
A wani taron manema labarai na murnar cikarsa shekaru 79, ya bukaci shugabannin PDP su magance matsalolin cikin gida a taron kasa na gaba.
"Yan Najeriya na jiran 2027" - Cif Bode
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Cif Bode ya ce akwai bukatar PDP ta dinke barakarta domin ceto Najeriya daga mawuyacin halin da APC ta jefa ta a yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cif Bode George ya ce 'yan Najeriya na jiran zaben 2027 ya zo domin korar Shugaba Bola Tinubu daga Villa, saboda gazawarsa a mulkin kasar.
Jagoran na PDP ya tabbatar da cewa jam'iyyarsu ce kadai za ta iya ceto Najeriya daga halin da ta shiga, yana mai cewa dole ne jam'iyyar ta sake inganta amana a cikin ta.
Ya jaddada cewa taron jam'iyyar da za a yi a Abuja ranar 28 ga Nuwamba yana da matukar muhimmanci wajen magance matsalolin PDP.
Cif Bode ya gano baragurbi a cikin PDP
Cif George ya yu gargadin cewa PDP na gab da shiga cikin babban rikici, yayin da ya gano wasu 'yan jam'iyyar da ke yi mata makarkashiya.
Ya zargi wasu daga cikin 'yan jam'iyyar da cin amanar PDP ta hanyar goyon bayan APC a cikin sirri, wanda ke kara haifar da rarrabuwar kai.
“Abin takaici ne yadda rashin amana ta yi katutu a PDP. Idan ba a magance wannan matsalar ba, za ta yi yin tasiri ga yunkurinmu na karbar mulki a 2027."
- A cewar Cif Bode George.
"Atiku ba zai samu tikiti ba" - Cif Bode
A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban PDP na kasa, Cif Bode George ya ce Atiku Abubakar ba zai samu tikitin takarar shugaban kasa a 2027 ba.
Cif Bode George ya ce dole Atiku Abubakar ya jira 2031 idan yana son sake neman zama shugaban ƙasa domin yanzu lokacin Kudu ne ta yi shugabanci na shekaru 8 jere.
Asali: Legit.ng