Gina Zauren Majalisa da Wani Aikin da Za Su Lakume Naira Biliyan 29 a Jihar Gombe
- Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kaddamar da ginin zauren majalisa da babban kotu, wanda zai ci N28.9bn
- An ce gine-ginen suna cikin shirin 'Three Arms Zone', wanda zai hada bangarorin zartarwa, dokoki, da shari’a a wuri guda
- Inuwa Yahaya ya ce gine-ginen za su karfafa dimokuradiyya, bunkasa shugabanci, da samar da yanayin aiki mai kyau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kaddamar da bikin ginin zauren majalisar dokoki da babbar kotun jihar a ranar Laraba.
Wadannan gine-gine suna cikin shirin 'Three Arms Zone', wanda zai hada hukumomin zartarwa, dokoki, da shari’a a wuri guda, a cewar gwamnan.
Gwamnatin Gombe za ta kashe N28.9bn
Jaridar Punch ta rahoto Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa kudin da za a kashe kan ayyukan zai kai Naira biliyan 28.9.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce gwamnatinsa na da muradin samar da yanayi mai kyau da zai baiwa dukkanin bangarorin gwamnati damar yin aiki yadda ya kamata.
Yayin bikin aza harsashin fara ayyukan, gwamnan ya ce:
“Tun kafuwar Gombe shekaru 28 da suka gabata, ba a taba samun wani yunƙuri irin wannan na inganta muhallin aiki ga ma'aikatan gwamnati da masu yiwa jama'a hidima ba.”
Amfanin gina majalisa da kotu a Gombe
Gwamnan ya kara da cewa gine-ginen za su kara karfafa tsarin mulki, bunkasa dimokuradiyya, da ci gaban al’ummar jihar baki daya.
Tun daga shekarar 2019, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce gwamnatinsa ta dage kan tabbatar da cin gashin kai ga bangaren majalisa da shari’a.
Ya ce ginin zai bude sabon babi na dangantaka tsakanin bangarorin gwamnati domin yin ayyukansu yadda ya kamata, a cewar rahoton Tribune.
"Wannan babban aiki ba wai iya aikin gina majalisa da kotun ba ne ba, wani ginshiki ne na samar da ci gaba a jihar ta hanyar inganta ayyukan bangarorin doka da shari'a."
A cewar gwamnan.
Gwamna zai rusa sabon gidan gwamnati
A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya yi alkawarin rusa sabon gidan gwamnati da aka gina na biliyoyin naira a Umuahia.
Tsohon gwamnan jihar Okezie Ikpeazu, ne ya kaddamar da sabon gidan gwamnatin ranar 28 ga watan Mayu, 2023 kwana daya kafin sauka daga mulki.
Asali: Legit.ng