Gwamna Zulum Ya Kara Yi Wa Ma'aikata Karin Albashi bayan Amincewa da N70,000

Gwamna Zulum Ya Kara Yi Wa Ma'aikata Karin Albashi bayan Amincewa da N70,000

  • Likitocin da ke aiki a ƙarƙashin gwamnatin jihar Borno za su samu ƙarin albashi daga ranar, 1 ga watan Disamban 2024
  • Gwamna Babagana Umar Zulum ya amince a yi musu ƙari su riƙa karɓar albashi daidai da wanda ke aiki da gwamnatin tarayya ke samu
  • Zulum ya umarci shugaban ma'aikatan jihar da kwamishinan lafiya su tabbatar an aiwatar da hakan ga likitocin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya amince da ƙarin albashi ga likitocin da ke aiki a ƙarƙashin gwamnatin jihar.

Gwamna Zulum ya amince a yi wa likitocin ƙari su koma suna karɓar albashi iri ɗaya da abinda ake biyan takwarorinsu a matakin tarayya.

Zulum ya yi karin albashi a Borno
Zulum ya yi wa likitoci karin albashi Hoto: Borno State Government
Asali: Facebook

Zulum ya yi wa likitoci karin albashi

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Zulum ya sanar da amincewar ne a jiya yayin da yake gabatar da jawabinsa a wani taro na majalisar harkokin lafiya ta ƙasa karo na 65.

Kara karanta wannan

Bauchi: Gwamna zai fara biyan sabon albashi da hakkokin ma'aikata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum ya umarci shugaban ma’aikata da kwamishinan lafiya su haɗa kai da hukumomin gwamnatin tarayya da abin ya shafa, domin cike giɓin da ke tsakanin abin da ake biyan likitocin da ke aiki a jihar da na gwamnatin tarayya.

Yaushe za a fara biya?

Gwamna Zulum ya ba da umarnin fara biyan ƙarin albashin daga ranar, 1 ga watan Disamba 2024, rahoton jaridar Businessday ya tabbatar.

"Ku yi aiki da hukumomin gwamnatin tarayya da abin ya shafa domin tabbatar da cewa babu bambance-bambance tsakanin albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya da masu aiki da gwamnatin jiha."
"Daga ranar 1 ga watan Disamba, likitocin da ke aiki da gwamnatin jihar Borno za su karɓi albashi daidai da na masu aiki da gwamnatin tarayya."

- Gwamna Babagana Umara Zulum

Zulum ya biya malaman makaranta sabon albashi

A wani labarin kuma, kun ji cewa malaman makarantun firamare a jihar Borno sun fara karɓar sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Malaman makarantun firamare a jihar sun yi murna a ranar Juma’a, 8 ga watan Nuwamba yayin da Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da aiwatar da mafi ƙarancin albashi na N70,000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng