Kwankwaso da Wasu Manyan Arewa da Suka Nuna Adawa da Kudirin Harajin Tinubu
- Tun a watan Satumba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura kudirin bukatar sauya fasalin harajin ga yan majalisar tarayya
- Daga lokacin kudirin ya fara shan suka wajen yan siyasa kasancewar wasu na zargin ba a musu adalci ba a cikin abin da kudirin ya kunsa
- A wannan rahoton, mun tatttaro muku wasu daga cikin shugabannin Arewa da suka nuna adawa da kudirin harajin Tinubu a bayyane
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kudirin haraji na Bola Tinubu na cigaba da shan suka yayin da ake tsammani nan gaba kadan majalisa za ta karanta shi.
Sai dai duk da shan suka da Tinubu ya yi kan kudirin, shugaban kasar ya ce ba zai janye shi daga majalisa ba.
A wannan rahoton mun tattaro muku jerin wasu shugabannin Arewa da suka soki kudirin harajin Bola Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Rabi'u Musa Kwankwaso
Sanata Rabi'u Kwankwaso ya nuna adawa da kudirin harajin Bola Tinubu inda ya ce ba a yi wa Arewa adalci ba.
Kwankwaso ya yi zargin cewa sabuwar dokar da ake shirin kawowa za ta fifita jihar Legas a kan wasu jihohin Najeriya.
"Muna sane da yadda mutanen Legas ke kokarin lafta mana haraji da kuma suke ƙoƙarin dauke haraji daga Kano da sauran jihohi zuwa Legas.
A yau, ko wayoyin hannu da muke kira da su a Kano ana so a dauke harajinsu zuwa Legas.
Bayan wasu cikin mutanenmu sun bude kamfanoni a Kano da jihohin Arewa, ana ƙoƙarin tilasta musu komawa jihar Legas."
- Sanata Rabi'u Kwankwaso
NAT ta yi martani ga Kwankwaso
Biyo bayan kalaman da Sanata Rabi'u Kwankwaso ya yi, wata kungiya mai goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ta masa martani.
Legit ta ruwaito cewa kungiyar NAT ta ce akwai alamar Kwankwaso bai fahimci abin da ya ke kunshe a cikin kudirin harajin ba.
Kungiyar ta zargi Kwankwaso da son siyasantar da kudirin musamman lura da yadda ya yi maganar a gaban daliban jami'ar Skyline ta Kano.
2. Sanata Ali Ndume
Daily Trust ta wallafa cewa Sanata Ali Ndume ya fito ƙarara ya ce ba zai goyi bayan kudirin haraji a majalisar dattawa ba.
Bayan haka, Ali Ndume ya yi alkawarin neman goyon bayan yan uwansa Sanatoci wajen yaki da kudirin idan aka gabatar da shi a gaban majalisar.
Dalilin da Ali Ndume ya ambata a kan kin kudirin shi ne har yanzu akwai matsalolin tsaro a yankunan Arewa kuma amincewa da kudirin zai jefa al'umma a karin wahala.
"Mutane suna fama da abin da za su ci, mutane suna fama da yadda za su rayu. A bari sai rayuwa ta yi kyau sai a fara maganar haraji."
- Ali Ndume
Shehu Sani ya saɓa da Ali Ndume
The Nation ta ruwaito cewa Sanata Shehu Sani ya saba da Ali Ndume kan kudirin sauya fasalin haraji na Tinubu.
Sanata Shehu Sani ya ce akwai abubuwa masu kyau da jihohi za su amfana da su a cikin kudirin harajin Tinubu.
Shehu Sani ya kara da cewa za a samu rage cin hanci da rashawa ta wasu ɓangarori idan aka tabbatar da kudirin.
"Daga cikin fa'idar da ke cikin kudirin akwai dokar da za ta ba kamfanoni damar ba jihohin harajin VAT maimakon tura shi ga asusun bai daya na gwamnatin tarayya.
Kudirin kokari ne mai kyau da zai taimaka wajen gyara yadda ake tattara haraji a Najeriya kuma zai taimaka wajen tara kudi ga kasa da jihohi.
Babu inda kudirin ya ce za a mayar da wani yanki baya ko kuma za a kara haraji ga jama'a ko rasa sana'o'i."
- Shehu Sani
3. Gwamnonin Arewa
Rahoton Arise News ya nuna cewa a wani taro da gwamnonin Arewa da sarakuna suka yi a jihar Kaduna sun nuna kin amincewa da kudirin harajin.
A karkashin haka, gwamnonin sun ce za su yi dukkan mai yiwuwa wajen yaki da kudirin idan Bola Tinubu bai janye shi ba.
Gwamnonin Arewa sun ce kudirin zai kara jefa jihohinsu a cikin matsalar tattalin arziki inda suka ce akwai tsare tsare da ba su gamsu da su ba.
Tinubu ya yi martani ga gwamnoni
Sai dai fadar shugaban kasa ta yi martani ga gwamnonin inda ta ce ba a kawo kudirin domin cutar da wani yanki ba.
Bayan haka, shugaba Bola Tinubu ya ce babu gudu ba ja da baya wajen gabatar da kudirin a gaban majalisar tarayya.
Shugaban kasar ya ce duk wani wanda yake son gyara zai iya tura buƙatarsa a lokacin da za a saurari ra'ayin jama'a kan kudirin.
Majalisar wakilai vs kudirin haraji
Kallo ya koma kan majalisar wakilai kan kudirin tun a lokacin da Bola Tinubu ya ce ba gudu ba ja da baya.
Daily Trust ta wallafa cewa mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu ya fadawa gwamnoni cewa har zuwa yanzu ba su fara aiki kan kudirin ba.
Benjamin Kalu ya ce za su yi nazari kan kudirin kuma za su tabbatar hukuncin da za su yanke ya zo daidai da ra'ayin yan kasa da suke wakilta
Gwamna ya ba Tinubu shawara kan haraji
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya yi magana kan yadda za a daidaita da Tinubu a kan kudirin haraji.
Gwamna Abdullahi Sule ya ce ba sa adawa da kudirin sai dai kawai suna so shugaba Bola Tinubu ya sauya wasu abubuwa ne kan harajin VAT.
Asali: Legit.ng