Tinubu na Brazil, Shettima Ya Dauki Matakan Kawo Karshen Lalacewar Wutar Lantarki

Tinubu na Brazil, Shettima Ya Dauki Matakan Kawo Karshen Lalacewar Wutar Lantarki

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya jagoranci taron majalisar tattalin arziki a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja
  • A yayin taron, majalisar tattalin arzikin ta amince da kafa kwamitin da zai yi aiki domin samar da wutar lantarki a kasar nan
  • Kashim Shettima ya yi karin haske kan ayyukan da kwamitin zai yi yayin da ya ce samar da wuta hakki ne na al'umma ba gata ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majalisar tattalin arziki ta kasa (NEC) ta dauki muhimman matakan kawo karshen durkushewar tashar wutar lantarki ta Najeriya.

A taronta na wata wata da ya gudana a fadar shugaban kasa a jiya Alhamis a Abuja, majalisar ta yanke shawarar aiwatar da tsarin wuta na kasa (NES).

Kashim Shettima ya yi magana yayin da majalisar NEC ta kafa kwamiti kan wutar lantarki.
Kashim Shettima ya jagoranci taron NEC, an kafa kwamitin aiwatar da gyara wutar lantarki. Hoto: @officialSKSM
Asali: Twitter

Shettima ya jagoranci taron NEC

Kara karanta wannan

Majalisa ta yi hukunci kan maida wa'adin shugaban kasa da gwamnoni shekara 6

Jaridar Daily Trust ta rahoto mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin ya na cewa wutar lantarki hakkin 'yan kasa ce.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima ya shaidawa 'yan majalisar cewa samar da wuta wani hakki ne ba gata ba saboda wutar lantarki iska ce ta ci gaban tattalin arziki.

Mataimakin shugaban kasar ya ce:

"A cikin 'yan watannin nan an samu yawaitar durkushewar tashar wutar lantarki wanda ya tilastamu daukar matakin aiwatar da tsarin wuta na kasa (NES).
"Samar da makamashi wani hakki ne na al'umma, ba wai gata ba. Makamashi ne iskar da tattalin arziki ke shaka yana samun bunkasa."

Majalisar NEC ta kafa kwamiti

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, shugaban majalisar tattalin arziki, ya sanar da kafa kwamitin mutum 13 kan aikin samar da wutar lantarki na kasa.

Kashim Shettima ya ce kwamitin karkashin gwamnan Cross Rivers, Bassey Otu zai taimaka wajen magance kalubalen da ake fuskanta a fannin wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya fadi halin da tattalin arziki ke ciki bayan fara mulkin Tinubu

Kwamitin zai yi aiki don zurfafa ayyukan jihohi a cikin dokar sake fasalin wutar lantarki na 2023 da kuma aiwatar da dabarun samar da wutar lantarki na kasa.

Najeriya ta shiga sabuwar kungiya a Brazil

A wani labarin, mun ruwaito cewa an fara ganin amfanin ziyarar da shugaban kasa Bola Tinubu ya kai kasar Brazil inda ya ke halartar taron shugabannin G20.

A yayin taron, Shugaba Tinubu ya sanya Najeriya cikin sabuwar kungiyar kawancen kasashen duniya da shugaban kasar Brazil ya kafa domin yaki da yunwa da talauci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.