Kungiyar ACF Ta Dakatar da Shugabanta bayan Kalamansa kan Zaben Tinubu a 2027

Kungiyar ACF Ta Dakatar da Shugabanta bayan Kalamansa kan Zaben Tinubu a 2027

  • Bayan sake bayanai kan zaben 2027 mai zuwa, Kungiyar Arewa Consultative Forum, ACF ta dakatar da shugabanta
  • An dakatar da Mamman Mike Osuman ne bayan ya yi wasu kalamai game da zaben 2027 inda ya ɗan yankin Arewa za su zaba
  • Osuman ya koka kan yadda tsare-tsaren Bola Tinubu suka rikita kasar musamman yankin Arewa da al'ummarta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta dakatar da shugabanta kan kalamansa a zaben 2027.

Kungiyar ta dauki matakin ne kan shugaban ACF, Mamman Mike Osuman kan katobarar da ya yi game da zaben 2027.

ACF ta dakatar da shugabanta bayan magana kan zaben Tinubu a 2027
Kungiyar Arewa Consultative Forum, ACF ta dakatar da shugabanta, Mamman Mike Osuman kan zaben 2027. Hoto: Arewa Consultative Forum, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: UGC

2027: ACF ta fadi wanda za ta zaba

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin amintattu, Alhaji Bashir Mohammed da sakataren ACF, Murtala Aliyu suka fitar, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

'Ko sai kowa ya mutu ne,' Dattawan Arewa sun yi raddi ga Tinubu kan tsadar rayuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan Osuman ya yi magana kan zaben 2027 da kuma takarar Shugaba Bola Tinubu.

A cikin sanarwar, Osuman ya ce yan Najeriya za su marawa dan takara daga Arewa ne kadai baya a zaben 2027 mai zuwa, Leadership ta ruwaito.

Musabbabin dakatar da shugaban ACF kan zaben 2027

"Mun samu bayanai kan abin da shugaban kungiyar ACF, Mamman Mike Osuman ya yi game da zaben 2027 yayin ganawar kwamitin zartarwa a jiya Laraba 20 ga watan Nuwambar 2024 a jihar Kaduna."
"An fitar da sanarwar ba tare da neman shawarar shugabannin kungiyar ba wanda hakan ke tabbatar da Osuman ya fadi ra'ayinsa ne."
"Shugabannin kungiyar ACF ta yi fatali da kalaman Mamman Mike Osuman gaba daya saboda haka ta dakatar da shi tare da kaddamar da bincike."

- Cewar sanarwar

ACF ta wanke Tinubu kan matsalolin Arewa

Kun ji cewa yayin da wasu ke zargin Shugaba Bola Tinubu kan matsalolin Arewa, kungiyar ACF ta yi martani mai tsauri kan matsalolin yankin.

Kara karanta wannan

'Ba laifinsa ba ne': Kungiyar ACF ta wanke Tinubu, ta fadi masu laifi a matsalolin Arewa

Shugaban kungiyar Arewa Consultative Forum, Mamman Mike Osuman ya ce matsalolin Arewa laifin shugabanninta ne.

Osuman ya ce ba za su daurawa Tinubu laifi ba kan abubuwan da ke faruwa duk da tsare-tsarensa ba su dace da yankin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.