Zanga Zanga : Gwamnatin Kano Ta Mika Yara 76 ga Iyayensu, an ba Kowane Yaro Tallafin Kudi
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta kammala duba lafiyar yaran nan da gwamnatin Tinubu ta daina shari'a da su kan cin amanar kasa
- An cafke yaran ne a sassa daban-daban na jihar Kano a lokacin zanga zangar kwanaki 10 da aka fara a ranar 1 Agusta, 2024
- Gwamnatu ta mika yaran ga iyayensu, bayan an kammala duba lafiyarsu na tsawon kwanai tare da ba su tallafi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta mika yaran Kano da aka karbo daga gwamnatin tarayya su 76 hannun iyayensu.
Gwamnatin Bola Tinubu ta garkame yaran na sama da watanni biyu bisa zargin tayar da husuma da yunkurin kifar da gwamnati lokacin zanga zanga.
Jaridar Leadership ta wallafa cewa a ranar Alhamis ne aka sallami yaran daga asibitin Muhammadu Buhari a Giginyu, inda ake duba lafiyarsu tun bayan dawowarsu gida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaran Kano sun koma ga iyayensu
Jaridar Daily News24 ta ruwaito cewa kwamishinan lafiya na Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya mayar da yaran da gwamnatin Tinubu ta daina shari’a da su ga iyayensu.
Dr. Labaran ya tabbatar da cewa an kammala duba lafiyarsu, kuma su na cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali, yayin da gwamnati ta ce za ta cigaba da bibiyarsu.
An ba yaran Kano kyautar kudi
Gidauniyar Bafarawa da ta halarci bikin mika yaran Kano da aka saki bayan zanga zanga, inda ta ba kowannensu kyautar N50,000 a matsayin tallafi.
Yaran guda 76 sun shaki iskar yanci ne bayan babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da tuhumar da gwamnati ke yi masu na cin amanar kasa.
Gwamna ya ja kunnen yaran zanga-zanga
A baya, mun ruwaito cewa gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya gargadi yaran nan da gwamnati ta janye tuhumar cin amanar kasa ake yi masu da su shiga hankalinsu daga yanzu.
Gwamna ya bayar da shawarar ne bayan an karbo su daga hannun gwamnatin tarayya, inda ya umarce su da su koma makaranta domin gina ingantacciyar rayuwa a nan gaba.
Asali: Legit.ng