IMF Ya Yi Baki Biyu, Ya Sake Matsaya kan Manufofin Tinubu 'Marasa Aiki'

IMF Ya Yi Baki Biyu, Ya Sake Matsaya kan Manufofin Tinubu 'Marasa Aiki'

  • Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya lashe amansa a kan yadda tattalin arzikin Najeriya ke cigaba a watanni 18
  • Rahoton da mataimakiyar shugaban IMF, Catherine Patillo ta gabatar a Legas ya nuna cewa an samu koma baya a kasar nan
  • A taron kasashen G20 da ke gudana a Brazil, Manajan Daraktar IMF, Kristalina Georgieva ta goyi bayan tsare-tsaren kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Brazil – Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya sake matsayar da ya bayyana a kan manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

A baya, wani rahoton da Asusun ya bayar kan cigaban tattalin arzikin Afrika ya nuna cewa Najeriya ba ta tabuka abin arziki ba a shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya fadi halin da tattalin arziki ke ciki bayan fara mulkin Tinubu

Tinubu
IMF ya goyi bayan tsare-tsaren Tinubu Hoto: @KGeorgieva
Asali: Twitter

Manajan Daraktar asusun IMF, Kristalina Georgieva a shafinta na X ta bayyana goyon baya ga kudurorin da gwamnatin Najeriya ke amfani da su wajen farfado da tattalin arziki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

IMF ya goyi bayan manufofin Bola Tinubu

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Manajan Darakta a asusun IMF, Kristalina Georgieva ta yabi tsare-tsaren gwamnatin Najeriya na samar da aikin yi da bunkasa tattalin arziki.

Ta fadi haka ne a taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G20 na kwanaki biyu da ke gudana a Rio de Janeiro a kasar Brazil a yanzu.

Asusun IMF ta yabi shugaba Tinubu

Mashawarcin shugaban kasa kan harkokin labarai, Bayo Onanuga ya tabbatar da cewa asusun IMF ya bayyana gamsuwa da tsare-tsaren gwamnatin Najeriya.

IMF ya nuna goyon bayansa ne a lokacin da kasar nan ta cire tallafi a bangarori da dama kamar na man fetur, wanda ya jawo matsin rayuwa da hauhawar farashi a kasuwanni.

Kara karanta wannan

Tinubu ya samo mafita kan yaki da ta'addanci a Afrika

IMF ta soki manufofin Tinubu

A wani labarin kun ji cewa asusun bayar da lamuni na IMF ya tabbatar da cewa tsare-tsaren gwamnatin Najeriya ba su yi tasirin da aka sa rai ba ta fuskar cigaban tattalin arziki.

Rahoton da mataimakiyar shugaban IMF, Catherine Patillo ta gabatar, ta nuna cewa Najeriya ba ta daga cikin kasashen da su ka samu bunkasar tattalin arziki kamar yadda aka yi hasashe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.