An Tsare Mutane 4 kan Taba Kimar Basarake saboda Zargin Yakar Musulunci
- Kotu ta tsare wasu mutane hudu kan neman bata sunan basarake da suke zargin yana neman haddasa fadan addini
- Kotun da ke Ibadan ta tsare mutanen ne da suka wallafa bidiyo a Facebook da ke bata sunan Soun na Ogbomoso, Oba Gandi Olaoye
- Sai dai wadanda ake zargin sun musanta tuhume-tuhumen da ake yi musu bayan karanto musu zargin da korafin basaraken
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Wasu mutane guda hudu sun gamu da fushin kotu bayan cafke su kan zargin bata sunan basarake.
Kotun Majistare da ke Iyaganku a Ibadan da ake jihar Oyo ta tsare wadanda ake zargin kan bata sunan Soun na Ogbomoso, Oba Ghandi Olaoye.
An kama mutane da zargin yi wa Sarki sharri
Leadership ta ce ana zargin mutanen hudu kan tuhume-tuhume guda uku inda suka wallafa bidiyo na batanci ga basaraken a kafofin sadarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda ake zargin sun hada da Owolabi Kazeem da Muritala Adebisi da Mustapha Abdulrahman da Abdulsalam Abdullahi.
Bayan karanto duka zarge-zargen da ake yi kansu, mutanen hudu sun ki amincewa da zargin.
Mutanen suna zargin Sarkin da yakar Musulmai
Dan sanda mai gabatar da kara, Akeem Akinloye ya ce wadanda ake zargin sun wallafa bidiyo da ke batanci ga Oba na Ogbomoso.
Akinloye ya ce mutanen sun wallafa bidiyo ne a Facebook da sauran kafafen sadarwa a ranar 25 ga watan Oktoban 2024 da misalin karfe 3.00 na rana.
Ya ce sun wallafa bidiyon inda suke zargin basaraken da hada rigima a tsakanin addinai guda biyu wanda sun san karya ne.
A bidiyon, sun zargi Sarkin da yakar Musulmai wanda ke kawo rashin zaman lafiya, cewar rahoton The Nation.
Kotu ta haramtawa basarake tsige limami
Kun ji cewa Babbar kotun jiha ta haramta basarake da 'yan majalisar masarautarsa daga tsige babban limamin Ogbomoso.
Mai shari'a K.B. Olawoyin ya kwaɓi sarkin Ogbomoso, Oba Afolabi Ghandi daga tuɓe rawanin Sheikh Teliat Yunus.
Wannan na zuwa ne bayan da masarautar Ogbomoso ta zargi Sheikh Teliat da zuwa aikin Hajji ba tare da izini ba.
Asali: Legit.ng