Mai Jego Ta Tsere daga Hannun yan ta'adda bayan An Kwace Jariranta

Mai Jego Ta Tsere daga Hannun yan ta'adda bayan An Kwace Jariranta

  • Ana zargin wasu yan bindiga da sace Maimuna, wata mata da ke dab da haihuwa a hanyar dawowa daga asibiti
  • Awanni bayan sace Maimuna, ta haihu a maboyar yan ta'addan, ta kuma haifo yan twagwaye guda biyu maza
  • Sai dai matar wacce ta gudo daga hannun miyagun ta bayyana cewa sun kwace jariran daga hannunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Niger - Wata mai juna biyu ta shiga tashin hankali bayan yan ta'adda sun sace ta a hanyar dawowa daga asibiti a jihar Neja.

Matar mai suna Maimuna mazauniyar garin Lambata ce a karamar hukumar Gurara a jihar Neja, ta fadi irin bakin cikin da ta shiga.

Niger
Yan ta'adda sun sace mai juna 2 a Neja Hoto: Legit.ng
Asali: Original

A labarin da ya kebanta da jaridar Aminiya, an sace matar da juna biyunta bayan ta je asibiti domin a duba lafiyarta.

Kara karanta wannan

Kano: Malamar da ta haura shekaru 20 ta na haura rafi don da'awa ta fara samun tagomashi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An haifi tagwaye a hannun yan ta'adda

Wata mata mai suna Maimuna ta bayyana cewa wasu yan bindiga sun sace ta bayan ta shiga motarsu daga babban asibitin garin Suleja zuwa Lambata.

Daga nan ne ta fita daga hayyacinta sai cikin dare ta farka bayan nakuda ta matsa, kuma ta haifi jarirai guda biyu.

Yan ta'adda sun kwace jarirai a Neja

Maimuna ta ce ta nemi jariranta ta rasa, duk da ta ji kukansu bayan haihuwarsu a maboyar yan ta'adda.

Daga bisani ta yi nasarar tserewa zuwa bakin titi, inda ta samu taimako daga wani bawan Allah direba.

Maimuna ta ce;

“A can ne na samu mota da za ta wuce da ni zuwa garin Minna, kuma mai motan ne ya taimaka mini ya tsaya a wani asibiti da ke wani kauye aka yi mini allura inda jinin da ke zuba ya ragu.
“Mun ci gaba da tafiya, sai dai bayan mun isa garin Zungero sai muka sami labarin cewa a kwai ɓarayi sun tare hanya ta gaba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano na shirin cika alkawari, an fara runtumo gagarumin aiki a bangaren ilimi

“Haka muka juya muka sake komawa garin Kagara, a can ne a ka kwantar da ni a wani asibiti tare da dora ni a kan ruwan leda da kuma ba ni magunguna."

Yan bindiga sun sace daliba

A baya mun ruwaito cewa wasu miyagun yan bindiga sun sace wata matashiya mai hidimar kasa (NYSC) Chiamaka Obi a hanyar Neja zuwa Onitsha bayan ta dawo daga jihar Kebbi.

Matashiyar 'yar asalin garin Edenta ne a Okwu Etiti, a karamar hukumar Orsu ta jihar Imo, kuma yan bindiga sun yi garkuwa da ita ne a ranar Litinin tare da neman makudan kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.