'Muna Goyon Bayanka': Malamin Musulunci Ya Magantu da Abba Hikima Ya Maka Wike a Kotu

'Muna Goyon Bayanka': Malamin Musulunci Ya Magantu da Abba Hikima Ya Maka Wike a Kotu

  • Fitaccen malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya yabawa lauya Abba Hikima
  • Assadus Sunnah ya ce suna goyon bayansa kuma ya kamata hukumomi su rika tantance mutane kafin kama su ba bisa hakkinsu ba
  • Malamin ya ce abin takaici ne yadda ake kama wadanda ba mabarata ba saboda sun yi shigar kaskanci duba da sana'o'insu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya yi magana kan matakin da lauya, Abba Hikima ya dauka a Abuja.

Shehin malamin ya yabawa gwazon lauyan inda ya ba sauran lauyoyi shawara kan goyon bayan Hikima a karar Nyesom Wike.

Sheikh Assadus Sunnah ya yabawa Hikima kan maka Wike a kotu
Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya yabawa lauya Abba Hikima da ya shigar da Nyesom Wike gaban kotu. Hoto: Abba Hikima, Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah, Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Wike: Assadus Sunnah ya yabawa Abba Hikima

Assadus Sunnah ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Sunnah ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Abba Hikima ya jagoranci maka Wike a kotu kan wulakanta yan Arewa a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shehin malamin ya koka kan yadda aka ruwaito cewa ana cin zarafin masu bara da marasa ƙarfi duk da cewa ba su goyon bayan bara sai da babban lalura.

Malamin ya ce mafi yawan matsalolin da ake samu daga shugabanni ne tushe wanda ya dagula kasar baki daya.

Assadus Sunnah ya fadi matsayarsa kan Abba Hikima

"Akwai wani Barista a Kano, Abba Hikima, dazu naga yana bayani cewa shi wannan mutumin Wike yana kokarin hana bara."
"Amma an fake da cin mutuncin mutane ko kai ba almajiri ba ne idan kana sana'a ko wani aiki daga nan shigarka kawai za a duba ka cancanci a barka ko a wulakanta ka."
"Kamar yadda ya fada a gabansa an kama wasu saboda yanayin shigarsu ko aikinsu inda suka maka wadanda ya kamata a kotu kuma muna goyon bayansu."
"Abin da ya yamutsa kasa kenan kama wanda bai yi laifi ba, ya kamata a rinka tantace mabaraci kafin daukar mataki kansa."

Kara karanta wannan

Bwala: An titsiye mai sukan Muslim Muslim da ya shiga gwamnatin Tinubu

- Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah

Dalilan Hikima na maka Wike a kotu

Kun ji cewa Barista Abba Hikima, babban lauyan nan mazaunin Kano da ke fafutukar kare hakkin dan Adam ya gano cin fuskar da ake yi wa yan Arewa.

Abba Hikima ya fadi haka ne bayan ikirarin da ya yi na cewa jami'an tsaro na azabtar da 'yan Arewa da sauran masu kananan sana'o'i a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.