'Ko sai Kowa Ya Mutu ne,' Dattawan Arewa Sun yi Raddi ga Tinubu kan Tsadar Rayuwa

'Ko sai Kowa Ya Mutu ne,' Dattawan Arewa Sun yi Raddi ga Tinubu kan Tsadar Rayuwa

  • Kungiyar dattawan Arewa ta ACF ta yi magana kan tsadar rayuwa da yan Najeriya ke cigaba da kuka a kai tun zuwan Bola Tinubu
  • Shugabannin kungiyar sun bukaci Bola Tinubu ya gaggauta sauya tsare tsaren da ya kawo domin ceto rayuwar miliyoyin yan Najeriya
  • A cewar kungiyar, ba a bukatar dogon nazari domin canza tsare tsaren lura da yadda suke barazana ga rayuwar yan kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Kungiyar dattawan Arewa ta ACF ta bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauya salon tafiyar da mulki.

ACF ta ce tsarin da Tinubu ya dauko ya na ruguza tattalin al'umma musamman masu kananan sana'o'i.

Tinubu
ACF ta bukaci Tinubu ya sauya salon tafiya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ACF ta yi magana ne bayan kammala wani taro da ta yi a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

'Ba laifinsa ba ne': Kungiyar ACF ta wanke Tinubu, ta fadi masu laifi a matsalolin Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ACF ta bukaci Tinubu ya sauya tsare tsare

Kungiyar ACF ta ce akwai bukatar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauya tsare tsaren tattalin arziki da ya kawo bayan hawa mulki.

Vanguard ta wallafa cewa ACF ta ce tsare tsaren na kara talauta al'umma da jefa su cikin tsananin rayuwa musamman a yankin Arewa.

A cewar ACF, farfaɗo da tattali abu ne mai muhimmanci amma bai kamata a jefa al'umma a wahala da sunan gyara ba.

"Tsare tsaren gwamnati suna cigaba da ruguza tattalin jama'a, kuma ba a lura da halin da aka jefa yan Arewa ba.
Bai kamata a kawo tsare tsaren tattalin da za su kara talauta al'umma ba. Ko sai mutane sun mutu ne za su amfana da tsare tsaren?"
Lura da halin da ake ciki, abin da ya fi dacewa shi ne sauya tsare tsaren gwamnati. Kuma a yanzu ya kamata a yi hakan."

Kara karanta wannan

'Miyagu sun yi ƙawanya ga Arewa,' ACF ta buƙaci koyar da dabarun kariya

- Kungiyar ACF

Kungiyar ta yi kira ga gwamnonin Arewa kan mayar da hankali wajen inganta Ilimi, kiwon lafiya noma, lantarki da koyar da sana'o'i.

ACF ta ce dole shugabannin Arewa su zauna cikin shiri domin fuskantar kalubalen kara yawan al'umma da yankin ke yi.

ACF za ta zabi dan Arewa a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Arewa Consultative Forum ta ce za ta zabi dan Arewa a zaben 2027.

Shugaban kungiyar ACF, Mamman Mike Osuman ne ya bayyana haka yayin wani taron da suka yi a jihar Kaduna a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng