'Ba Laifinsa ba ne': Kungiyar ACF Ta Wanke Tinubu, Ta Fadi Masu Laifi a Matsalolin Arewa
- Yayin da wasu ke zargin Shugaba Bola Tinubu kan matsalolin Arewa, kungiyar ACF ta yi martani mai tsauri kan matsalolin yankin
- Shugaban kungiyar Arewa Consultative Forum, Mamman Mike Osuman ya ce matsalolin Arewa laifin shugabanninta ne
- Osuman ya ce ba za su daurawa Tinubu laifi ba kan abubuwan da ke faruwa duk da tsare-tsarensa ba su dace da yankin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta yi magana kan matsalolin yankin Arewa.
Kungiyar ta wanke Shugaba Bola Tinubu kan matsalolin yankin inda ta ce laifin shugabanninta ne.
ACF ta zargi shugabannin Arewa kan matsalolinta
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugabanta, Mamman Mike Osuman ya fitar a yau Laraba 20 ga watan Nuwambar 2024, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar ACF, Osuman ya tabbatar da cewa shugabannin yankin sun ba da gudunmawa wurin kawo matsala ba kawai laifin Tinubu ba ne.
Sai dai ya amince da cewa akwai wasu matakai na Tinubu da ba su dace da yankin ba kwata-kwata, Leadership ta ruwaito.
Kungiyar ACF ta magantu kan tsare-tsaren Tinubu
"Na amince cewa akwai wasu tsare-tsare na gwamnatin Tinubu da suka saba da yankin Arewacin Najeriya."
"ACF ta yi imanin cewa wasu tsare-tsaren da kuma halayen shugabannin yankin yana bukatar sake duba a kai."
"Akan haka ne muke tambayar shin yaushe shugabanninmu za su nuna damuwa kan matsalolin da yankin ke ciki."
"Yaushe gwamnoninmu da yan Majalisu za su hada kai domin kawo karshen abubuwan da ke faruwa da aikata laifuffuka da matsanmu ke yi?"
- Mamman Mike Osuman
Tinubu ya bukaci kawo karshen matsalolin Arewa
Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga shugabannin Arewa da su fadada tunani domin gano maganin matsalolin da ke damun yankinsu.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa kan ci gaban matasan Arewa da gidauniyar Ahmadu Bello ta shirya.
Shugaban kasar ya ce idan shugabanni suka dukufa za su iya nemo mafita ga matsalolin Arewa domin ba abin wahala ba ne.
Asali: Legit.ng