Uba Sani Ya Fadi Muhimmin Abin da Zai Taka Rawa Wajen Magance Rashin Tsaro a Arewa

Uba Sani Ya Fadi Muhimmin Abin da Zai Taka Rawa Wajen Magance Rashin Tsaro a Arewa

  • Gwamnan jihar Kaduna ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar rashin tsaro ta maida yankin Arewacin Najeriya koma baya a ƙasar nan
  • Uba Sani ya yi kira ga gwamnatocin jihohin Arewa da su riƙa sanya matasa a cikin shirye-shiryen ganin an magance matsalar
  • Gwamnan ya bayyana cewa sanya matasa a ciki zai yi tasiri sosai wajen magance matsalar wacce ta daɗe tana addabar yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ta addabi yankin Arewacin Najeriya.

Gwamna Uba Sani ya yi kira da a riƙa sanya matasa a dabarun yaƙi da rashin tsaro a Arewa.

Uba Sani ya magantu kan rashin tsaro a Arewa
Uba Sani ya nuna damuwa kan rashin tsarona Arewacin Najeriya Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Uba Sani ya bayyana hakan ne a Kaduna ranar Laraba a taron masu ruwa da tsaki kan ci gaban matasan Arewacin Najeriya wanda gidauniyar Sir Ahmadu Bello ta shirya, cewar rahoton jaridar The Cable.

Kara karanta wannan

"Ku nemo maganin matsalolin yankinku" Tinubu ya aika sako ga shugabannin Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Uba Sani ya ce kan rashin tsaro?

Gwamna Uba Sani ya ce ƴan ta’adda da masu tada ƙayar baya sun yi wa matasa illa sosai, wanda hakan ya sa yankin Arewa kasa samun ci gaba.

"Dole ne gwamnatocin jihohin Arewa su sanya matasa a cikin tsare-tsaren samar da tsaro."
"Shigarsu a ciki zai taka muhimmiyar rawa a yaƙin da muke yi da matsalar rashin tsaro da magance matsalolin rashin ci gaba da suka addabe mu."
"Yayin da sauran yankuna suka mayar da hankali wajen magance ƙalubalen ci gaba da kyautata rayuwar mutanensu, ta'addanci, garkuwa da mutane, ƴan bindiga da masu tada ƙayar baya sun maida Arewa koma baya."

- Uba Sani

Gwamnan ya yi nuni da cewa kafin shekarar 2016, mutane na yin zirga-zirga ba yare da fargabar za a kai musu hari ba a yankin Arewacin Najeriya.

Gwamnati ta ɓullo da dabara kan rashin tsaro

Kara karanta wannan

Durkusar da Arewa: Sabon Ministan Tinubu ya yi wa Kwankwaso martani, ya gargade shi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bijiro da wata manhaja da za ta ba wa yan kasa damar mika sakon ta'addanci ko rashin tsaro a yankunansu.

Gwamnatin ta bayyana cewa manhajar da aka ba sunan 'mobilizer' za ta taimakawa jami'an tsaro wajen samun bayanai tare da daukar matakan dakile ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng