Bauchi: Gwamna Zai Fara Biyan Sabon Albashi da Hakkokin Ma'aikata

Bauchi: Gwamna Zai Fara Biyan Sabon Albashi da Hakkokin Ma'aikata

  • Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya sanya lokacin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata
  • Sanata Bala Muhammad ya ce a shirye yake ya biya dukkan ma'aikatan jihar da suka gama aiki hakkokinsu lura da halin tsadar rayuwa da ake ciki
  • Gwamnan ya kara da cewa ƙididdigar da aka fitar a kan cewa akwai talauci sosai a Bauchi ta zaburar da shi wajen yaki da fatara a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya ce a watan Nuwamba zai fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi.

Gwamnan ya ce mutane suna fama da wahalar rayuwa saboda haka akwai buƙatar gwamnati ta tausaya musu.

Bala Muhammad
Za a fara biyan sabon albashi a Bauchi. Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Twitter

Legit ta tatttaro bayanan ga gwamnan ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Laraba.

Kara karanta wannan

Ma'aikata sun yi barazanar shiga yajin aiki a Arewacin Najeriya, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bauchi: Za a fara biyan sabon albashi

Gwamnan jihar Bauchi ya amince da fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi a karshen watan Nuwamba.

Sanata Bala Muhammad ya yi alkawarin ne bayan zaman majalisar zartarwar jihar a yau Laraba, 20 ga watan Nuwamba.

Gwamna zai biya hakkokin ma'aikata

Sanata Bala Muhammad ya yi alkawarin biyan dukkan hakkokin ma'aikatan da suka gama aiki a Bauchi.

Gwamnan ya roki tsofaffin ma'aikatan da su cigaba da hakuri domin gwamnati na kan ƙoƙarin biyansu harkokinsu.

NBS ta ce akwai talauci a Bauchi

Sanata Bala Muhammad ya ce cibiyar ƙididdiga ta NBS ta yi rahoto kan cewa jihar Bauchi na cikin jihohi masu fama da talauci sosai a Najeriya.

A karkashin haka, Bala Muhammad ya ce rahoton ya zamo kalubale a garesu wajen bukatar ninka kokari da ya kamata su yi.

Gwamna Bala Muhammad ya ce za su cigaba da ƙoƙarin tabbatar da cewa mutanen Bauchi sun sharɓi romon dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sanar da sabon albashin da zai fara biyan ma'aikata, ya yi ƙarin fansho

Bala Muhammad ya soki Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa wamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya bukaci gwamnatin tarayya da ta rika fitar da bayanai kan raba arzikin kasa.

Bala Muhammad ya zargi gwamnatin karkashin Bola Tinubu da yi wa yan kasar nan rufa rufa kan yadda ake raba arzikin Najeriya ga jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng