Kudirin Sabuwar Dokar Zabe Ya Tsallake Karatu na 2 a Majalisa
- Majalisar wakilai ta yi karatu na biyu ga kudirin dokar da zai ba yan Najeriya da ke zaune a ƙasashen ketare damar yin zaɓe
- Tun a watan Juli majalisar ta yi karatu na farko ga kudirin da shugabanta, Abbas Tajudeen da Sodeeq Abdullahi suka gabatar
- Yan Najeriya sun dade suna bukatar kawo sauyi ga dokar zaben Najeriya musamman wadanda suka zaune a kasashen waje
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar dokokin Najeriya ta yi karatu na biyu ga kudirin da zai kawo sauyi a harkokin zabe.
Rahotanni sun nuna cewa kudirin dokar da ake kokarin kawowa zai ba yan Najeriya da ke kashen waje damar kada kuri'a yayin zabe.
Rahoton Channels Television ya nuna cewa a yau Laraba, 20 ga watan Satumba majalisa ta yi karatu na biyu ga kudirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karatun kudirin dokar zabe na farko
Tun a watan Yuli majalisar dokokin Najeriya ta yi karatu na daya ga kudirin dokar da zai ba mazauna kasashen waje damar yin zabe.
Bayan kammala karatun aka mika kundin kudirin ga kwamiti mai lura da harkokin zabe domin yi masa bahasi na musamman.
An yi karatu na 2 ga kudirin zabe
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa zaman majalisar dokokin Najeriya na yau Laraba aka sake karatu ga kudirin dokar.
Bayan karatu na biyu, majalisar ta mika kudirin ga kwamiti mai lura da harkokin sauya dokokin kasa domin yin nazari a kansa.
Waɗanda suka gabatar da kudirin
A watan Yuli shugaban majalisar dokokin Najeriya, Abbas Tajudeen ya gabatar da kudirin ga majalisa.
An ruwaito cewa shugaban majalisar ya yi haɗaka ne da Hon. Sodeeq Abdullahi wajen gabatar da shi.
Kudirin zai kawo gyara ga dokar zabe ta 2022 ta inda yan Najeriya da ke kasashen waje za su samu damar kada kuri'a yayin zabe.
Yan majalisa sun soki kudirn haraji
A wani rahoton, kun ji cewa kudirin haraji da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aikawa majalisa ya cigaba da jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al'umma .
An ruwaito cewa yan majalisar tarayya da suka fito daga Arewacin Najeriya sun bayyana illar da kudirin zai haifar a yankunansu.
Asali: Legit.ng