Gwamnatin Tarayya Ta Kori Shugaban Babbar Jami'a, Ta Fadi Dalili
- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da korar shugaban jami'ar Nnamdi Azikiwe (UNIZIK) da ke jihar Abia
- Ma'aikatar ilmi ta tarayya ce ta bayyana korar Farfesa Bernard Odoh kan abin da ta kira naɗa shi ba bisa ƙa'ida ba
- An kuma rusa majalisar gudanarwa ta jami'ar bisa zargin ta da laifin bin umarnin ma'aikatar ilmi ta tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ma’aikatar ilimi ta tarayya ta sanar da tsige sabon shugaban jami’ar Nnamdi Azikwe (UNIZIK), Farfesa Bernard Odoh.
Ma'aikatar ilmin ta kuma sanar da rusa majalisar gudanarwa ta jami'ar.
An saɓa doka a jami'ar UNIZIK
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa ranar Laraba mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ma’aikatar ilimi, Folashade Boriowo, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙungiyar ASUU ta zargi majalisar gudanarwa ta jami'ar da rashin bin ƙa’idojin da suka dace wajen naɗa Bernard Odoh, sannan ta buƙaci ma'aikatar ilmi da ta rusa ta saboda ayyukan da suka saɓawa doka.
Meyasa gwamnati ta kori shugaban jami'a
"Gwamnatin tarayya ta sanar da rusa majalisar gudanarwa ta jami’ar Nnamdi Azikiwe da ke Awka a jihar Anambra, sakamakon saɓa dokokin jami’ar da kuma rashin bin umarnin ma’aikatar ilimi ta tarayya."
"An ɗauki matakin ne ne bayan da aka gano cewa shugaban majalisar a ƙashin kansa ya naɗa shugaban jami'ar wanda bai cika ƙa'idojin samun muƙamin ba."
"Hakan ya haifar da taɓarɓarewar doka da oda a jami’ar, lamarin da ya haifar da tashin hankali da rashin jituwa."
"Mai girma ministan ilimi ya kuma sanar da korar Farfesa Bernard Odoh, shugaban jami’ar da rusasshiyar majalisar gudanarwa ta jami’ar Nnamdi Azikiwe ta naɗa ba bisa ƙa’ida ba."
- Folashade Boriowo
Jami'a ta kori malamai
A wani labarin kuma, kun ji cewa Kwamitin gudanarwar jami’ar tarayya ta Lokoja (FUL) da ke jihar Kogi ya amince da korar wasu malamai hudu kan zargin lalata da dalibai.
Karkashin jagorancin Victor Ndoma-Egba, kwamitin ya yanke wannan hukunci a taronsa na biyu, domin tabbatar da da'a tsakanin malaman jami’ar.
Asali: Legit.ng