Majalisar Dattawa Ta Gano Mafita kan Ayyukan Yan Ta'addan Lakurawa a Jihohi 2
- Majalisar dattawa ta bukaci sojoji su haɗa kai da mazauna yankuna domin kawo karshen ayyukan ƙungiyar Lakurawa
- A zaman ranar Laraba, 20 ga watan Nuwamba, majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta kawar da ƙungiyar tun kafin ta mamaye Arewa
- Wannan dai na zuwa ne bayan ƴan Lakurawa sun kai wani mummunan hari kauyen Mera a jihar Kebbi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta shawarci rundunar sojojin Najeriya ta haɗa kai da mutanen da ke zaune a garuruwan da ake fama da hare-haren ta'addanci.
Majalisar ta bukaci sojojin su haɗa kai da mazauna irin waɗannan yankuna domin kafa wani tsari na gano shirin miyagu tun kafi su kai da kawo hari.
Channels tv ta ce majalisar ta ba da wannan shawara ne bayan tattaunawa kan ƙorafin da Sanata Yahaya Abdullahi (Kebbi ta Arewa) ya gabatar a zaman yau Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar dattawa ta magantu kan Lakurawa
Sanatan dai ya jawo hankalin majalisar kan ayyukan kungiyar ƴan tada kayar baya watau Lakurawa a wasu sassan jihohin Sakkwato da Kebbi.
A harin baya-bayan nan da suka kai jihar Kebbi ranar 8 ga watan Nuwamba, ƴan ta'addan Lakurawa sun kashe sojoji takwas a kauyen Mera, rahoton Vanguard.
A yayin muhawara kan batun, 'yan majalisar sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki kwararan matakai don daƙile kai hare-hare da hana yaɗuwar ƙungiyar.
Majalisa ta gargaɗi gwamnatin tarayya
Sanatocin sun yi gargadin cewa rashin daukar matakin da ya dace zai iya baiwa kungiyar Lakurawa damar fadada ayyukanta na ta’addanci a wasu sassan Arewa.
Bugu da ƙari, majalisar dattawan ta bukaci gwamnati ta tura tawaga zuwa yankin da aka kai hari a Kebbi domin tantance ɓarnar da ƴan ta'addan suka yi.
Ta kuma umarci dakarun sojoji su shiga cikin waɗannan yankuna domin hana Lakurawa ci gaba da kai hare-hare da kuma yaɗa mummunar aƙidarsu.
Ƴan Lakurawa sun ji ruwan wuta
A wani rahoton, kun ji cewa hukumomin tsaron kasar nan sun durfafi tarwatsa kungiyar yan ta'addan Lakurawa da su ka kutso Najeriya.
Dakarun sojin sama da na kasa sun yi wa Lakurawan da ke da sansani a Kebbi ruwan wuta, wanda ya sa suka arce suka bar yankin.
Asali: Legit.ng