Turji Ya Bani: Mukaddashin Hafsan Sojoji Ya Magantu, Ya Fadi Illar da Zai Yi Musu
- Sabon mukaddashin hafsan sojoji a Najeriya, Laftanar-janar Olufemi Oluyede ya sha alwashin kakkabe yan ta'adda gaba daya
- Laftanar-janar Olufemi ya bukaci yan ta'adda su shirya domin a wannan lokaci ba za su ji ta dadi ba ko kadan karkashin ikonsa
- Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan bikin binne marigayi tsohon haifsan sojoji, Laftanar-janar Taoreed Lagbaja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Mukaddashin hafsan sojojin Najeriya, Laftanar-janar Olufemi Oluyede ya magantu kan yan ta'adda.
Laftanar-janar Olufemi ya ce ko kadan ba zai sassautawa yan ta'adda ba a kasar inda ya gargade su kan ayyukan ta'addanci da suke yi.
Hafsan sojoji ya yi gargadi ga yan ta'adda
Mukaddashin hafsan sojojin ya bayyana haka ne a yau Laraba 20 ga watan Nuwambar 2024 a Kaduna, cewar rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Laftanar-janar Olufemi ya ce yan ta'adda da sauran masu aikata laifi za su fuskanci ukuba daga rundunar sojoji ba tare da sassautawa ba.
"Ina gargadin yan ta'adda da su shirya a wannan lokaci saboda za su fuskanci ukuba daga rundunar sojoji babu kakkautawa."
"Yan Najeriya kuma na yi musu alkawari karkashin iko na za mu tabbatar mun samar musu da tsaro mai inganci da kwanciyar hankali."
- Laftanar-janar Olufemi Oluyede
Hafsan sojoji ya nada sabon kwamandan rundunar
Hafsan sojojin ya bayyana haka yayin mika ragamar mukamin kwamandan sojojin Najeriya a Kaduna ga Manjo-janar Abdul-Khalifa Ibrahim.
Kafin nada Olufemi mukaddashin hafsan sojojin, shi ne kwamandan sojojin na 56 a jihar Kaduna.
Sojoji sun yi ruwan bama-bamai kan yan ta'adda
Kun ji cewa dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun samu nasarar kai hare-hare kan ƴan bindiga a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya.
Gwarazan sojojin sun yi ruwan wuta daga sararin samaniya kan ƴan bindiga a ƙauyen Babban Kauye na ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar.
Hare-haren na sama da aka kai kan ƴan bindigan masu shirin kai hari ga sojoji, sun yi sanadiyyar hallaka miyagu da dama.
Asali: Legit.ng