Kwamitin Binciken Gobarar Tankar Fetur a Jigawa Ya Mika Rahotonsa ga Gwamnati
- Gwamnatin Jigawa ta karbi rahoton kwamitin da ta kafa domin binciken matsalar faduwar tankar fetur a jihar
- Shugaban kwamitin, DIG Hafiz Muhammad Inuwa mai ritaya ya shaidawa Legit cewa sun bayar da shawarwari
- Daga cikin abin da su ka bukaci gwamnati ta yi akwai tabbatar da tankokin fetur na dauke da abin hana mai zuba idan ta fadi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Jigawa – Kwamitin da gwamnatin Jigawa ta kafa don binciken faduwar tankar fetur da ta fadi a jihar tare da lakume rayukan daruruwan jama’a ya mika rahotonta.
A rahoton da kwamitin ya mikawa gwamna Umar Namadi a ranar Laraba, an gano adadin wadanda su ka rasu ya kara hawa fiye da da.
TVC News ta wallafa cewa haka kuma rahoton ya fadi adadin mutanen da su ka samu lafiya tare da komawa ga iyalansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamitin Jigawa ya mika rahoto ga gwamna Namadi
Rahoton kwamitin binciken faduwar tankar fetur a Jigawa kan faduwar tanka a Majiya, karamar hukumar Taura ya nuna cewa mutane 209 ne su ka rasu a iftila’in da ya jijjiga jihar.
Mutane 38 ne har yanzu ke kwance a gadon asibitin, yayin da wasu mutum 86 su ka samu sauki, har sun koma gida.
Gwamnan jihar, Umar Namadi ya bayyana cewa zai yi amfani da dukkan shawarwarin kwamitin da ke kunshe a cikin rahoton.
Shawarar kwamitin Jigawa kan faduwar tankar fetur
Shugaban kwamitin, DIG Hafiz Muhammad Inuwa mai ritaya ya shaidawa Legit cewa sun mika shawarwari ga gwamnatin Jigawa kan iftila’in domin kare rayuka a nan gaba.
DIG Hafiz Muhammad Inuwa mai ritaya ya shaida cewa;
“Daya daga cikin shawarwarin shi ne tabbatar da cewa an samar da wajen kula da irin wadannan motoci na dakon mai, a tabbatar da cewa a ko da yaushe motocin su na dauke da abin da zai hana fetur zubewa idan tanka ta fadi.”
DIG Inuwa mai ritaya ya kara da cewa bincikensu ya tabbatar masu wasu motocin ba su da irin wannan abin kariya, wanda ya kara ta’azzara iftila’in.
Shugaban kwamitin ya kara da cewa;
“Mun ba da shawarar cewa a samar da wuraren da su ke kawo agaji na gaggawa idan irin wannan abubuwan sun faru, a ba su kulawa ta musamman.”
Sauran shawarwarin da kwamitin ya bayar sun hada da samar da hukumar kula da sufuri da gina wuraren kula da kuna da lafiyar kwakwalwar marasa lafiya.
Tankar fetur ta sake faduwa a Jigawa
A wani labarin, kun ji cewa hukumomi a Jigawa sun tabbatar da faduwar wata tankar fetur a safiyar Talata, bayan faduwar wata tankar da ta lakume rayukan mutane sama da 200.
Kakakin hukumar kashe gobara ta kasa a Jigawa, Auwal Muhammad Abdullahi shi ne ya tabbatar da afkuwar hadarin, amma ya ce ba a samu asarar rai ko guda daya ba.
Asali: Legit.ng