'Na Yi Babban Rashi': Buhari Ya Jajanta da Amininsa, Talban Katsina Ya Kwanta Dama

'Na Yi Babban Rashi': Buhari Ya Jajanta da Amininsa, Talban Katsina Ya Kwanta Dama

  • Kwanaki ƙadan da rasuwar Talban Katsina, Ambasada Zakari Ibrahim, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi alhini
  • Buhari ya ce ya yi babban rashin amini wanda suka zauna aji daya tare a makaranta inda ya ce tabbas an rasa hazikin mutum mai amfani
  • Wannan na zuwa ne bayan rasuwar tsohon shugaban hukumar NIA wanda ya rike muƙamin shugabancinta daga shekarar 1993 zuwa 1998

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar amininsa a jihar Katsina.

Buhari ya jajantawa iyalan marigayi Talban Katsina kuma tsohon shugaban hukumar NIA, Ambasada Zakari Ibrahim.

Buhari ya miƙa sakon ta'azziya ga iyalan Talban Katsina
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan marigayi Talban Katsina, Ambasada Zakari Ibrahim. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Getty Images

Buhari ya kadu da rasuwar Talban Katsina

Tsohon shugaban kasar ya yi ta'azziyar a yau Laraba 20 ga watan Nuwambar 2024 a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya bukaci Tinubu ya kori shugaban INEC Mahmood Yakubu, ya ba da dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya ce tabbas an yi rashin mutumin kirki da ya ba da gudunmawa sosai wurin tabbatar da inganta tsaro a lokacinsa har ma bayan ya bar aiki.

Har ila yau, Buhari ya jajantawa Gwamna Umaru Dikko Radda da Sarkin Katsina, Mai Martaba Abdulmuminu Kabir Usman da al'ummar jihar kan wannan babban rashi da aka yi.

Ya ce rashin Talban Katsina ya shafe shi a matsayinsa na amininsa sannan jihar da kasa baki sun tafka asara.

Buhari ya bayyana gudunmawar da marigayin ya bayar

"Tun farkon fara aikinsa, ambasada Zakari ya himmatu wurin tabbatar yin aikinsa tukuru."
"Yana da kwarewa a fanninsa da mayar da hankali kan abubuwa masu muhimmanci da kuma gudanar da wasu ayyuka da ke da hatsari."
"Rashinsa ya jawo babban asara ga hukumar leken asiri ta kasa, ina addu'ar Allah ya gafarta masa."

- Muhammadu Buhari

Talban Katsina, Ambasada Zakari Ibrahim ya rasu

Kara karanta wannan

Babban Malami na 3 ya rasu a Arewa cikin kasa da mako 1

Kun ji cewa an yi babban rashi a jihar Katsina bayan rasuwar tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta ƙasa (NIA).

Ambassada Ibrahim Zakari ya yi bankwana da duniya ne yana da shekara 81 a duniya a ranar Lahadi, 17 ga watan Nuwamban 2024.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya nuna alhininsa kan rasuwar marigayin wanda yake riƙe da sarautar Talban Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.