"Ku Nemo Maganin Matsalolin Yankinku" Tinubu Ya Aika Sako ga Shugabannin Arewa

"Ku Nemo Maganin Matsalolin Yankinku" Tinubu Ya Aika Sako ga Shugabannin Arewa

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga shugabannin Arewa da su fadada tunani domin gano maganin matsalolin yankinsu
  • Tinubu ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa kan ci gaban matasan Arewa da gidauniyar Ahmadu Bello ta shirya
  • Shugaban kasar ya ce idan shugabanni suka dukufa za su iya nemo mafita ga matsalolin Arewa domin ba bun wahala ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga shugabannin Arewa da su nemo hanyoyin magance matsalolin yankin.

Tinubu ya yi wannan kiran ne a taron tattaunawa kan ci gaban matasan Arewa da gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya a Abuja.

Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan hanyoyin magance matsalolin Arewa
Shugaba Tinubu ya aika sako ga shugabannin Arewa kan magance matsalolin yankin. Hoto: @officialSKSM
Asali: Twitter

Tinubu ya fadi amfanin ci gaban Arewa

Taron ya mayar da hankali ne kan batun “Karfafawa matasa don ci gaba mai dorewa a Arewacin Najeriya,” a cewar rahoton PM News.

Kara karanta wannan

'Idan babu Arewa, babu Najeriya,' Tinubu ya ce gwamnati za ta bunkasa rayuwar matasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasar ya ce manufofin Sir Ahmadu Bello sun fayyace cewa ci gaban Arewa yana da matukar muhimmanci wajen samun bunkasar Najeriya baki daya.

Da ya samu wakilcin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ba za ta bunƙasa ba sai kowanne yanki ya samu ci gaba.

“Idan yanki daya ya samu tsaiko a ci gaba, to hakan yana shafar dukannin kasar.”

- A cewar Tinubu.

"Mu fadada tunani" - Sakon Tinubu ga Arewa

Shugaban ya kara da cewa idan shugabanni suka dukufa za su iya lalubo mafita ga matsalolin yankin Arewa domin hakan ba abu mai wahala ba ne.

Kamfanin dillancin Labarai na kasa NAN ya ruwaito Tinubu na cewa:

"Akwai bukatar mu a matsayinmu na shugabanni mu fadada tunani wajen samar da mafita ga matsalolin Arewacin Najeriya, hakan bai fi karfinmu ba.
"Wannan dalilin ne ya sa gwamnati ta samar da hukumar almajirai da yara marasa zuwa makaranta domin ganin kowanne yaro ya samu ilimi mai nagarta. "

Kara karanta wannan

"A yi mana bayanin yadda ake raba arzikin kasa," Gwamnan PDP ya taso Tinubu

Tinubu ya kara jaddada bukatar zuba jari a fannin ilimin matasa, yana mai cewa, “idan muka kula da su yanzu, to suma za su kula da mu nan gaba.”

Tinubu ya gano abin da ya ruguza Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ce matsalar tsaro ce babbar abin da ta jawo rugujewar mafi yawan garuruwan Arewa.

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta gano cewa kawo karshen matsalar tsaro a Arewa na bukatar waiwayar baya saboda rashin adalci da ya farraka al'umomi da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.